Rundunar sojin sama ta lalata hedikwatar tsare-tsaren kungiyar ISWAP a Kollaram, Borno

Rundunar sojin sama ta lalata hedikwatar tsare-tsaren kungiyar ISWAP a Kollaram, Borno

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta bayyana cewa dakaruta dake gudanar da aikin Operation Lafiya dole sun tarwatsa hedikwatan tsare-tsare na kungiyar yan ta’addan ISWAP a Kollaram da ke yankin Arewacin Borno.

Air Commodore Ibikunle Daramola, Darektan Sadarwa da yada labarai na NAF, ya bayyana haka a wani jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, a Abuja.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa dakarunta sun gudanar da aikin ne a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni.

“Rundunar Sojin saman Najeriya (NAF), ta hannun Air Task Force (ATF) na Operation lafiya dole, ta kaddamar OPERATION GREEN SWEEP 2 akan kungiyar yan ta’addan a yankin Arewa maso gabashin kasar.

“Aikin rundunar sojin saman da aka fara a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, zata zabi wurare a cikin yankin Arewa maso Gabas don cigaba da tarwatsa sauran yan ta’addan da sansaninsu.”

KU KARANTA KUMA: Ku fada mun kalubalen da kuke fuskanta a filin daga – Buratai ya bukaci sojoji

Kakakin rundunar yayi bayanin cewa an kaddamar da harin ne bayan rangaji daban-daban da sashin kwararru suka gudanar.

Yace binciken ya nuna bayyanar wasu adadi na mayakan ISWAP a gine-ginen da ke karkashin bishiyoyi da suka yadu a wajen da kuma wasu ramuka masu zurfi a wurare daban-daban.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng