Ku fada mun kalubalen da kuke fuskanta a filin daga – Buratai ya bukaci sojoji

Ku fada mun kalubalen da kuke fuskanta a filin daga – Buratai ya bukaci sojoji

- Laftanal Janar Tukur Buratai ya tambayi sojojin Operatio Lafiya Dole da su fada masa matsalolin da suke fuskanta a filin daga

- Janar Buratai wanda ya kasance Shugaban hafsan soji, ya zanta da dakarun soji a Maiduguri, jihar Borno, a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni

- Buratai yace an inganta jin dadin sojoji idan aka hada da yadda abun yake a 2015, cewa a shirye yake ya kara kokari a kai

Shugaban rundunan soji, Laftanal Janar Tukur Burataia jiya Laraba, 26 ga watan Yuni a Maiduguri, jihar Borno ya gana da rundunan sojin Operation Lafiya Dole inda ya bukacesu da su fada mishi kalubalen da suke fuskanta a filin daga.

Buratai yace an inganta fannin more rayuwa na rundunar idan aka kwatanta da na 2015, inda yake fadin cewa a shirye yake don yin fiye da haka.

“Akwai muhimman al’amura kamar more rayuwa, kayan aiki, gudanarwa, dabaru da dukkan kwamandoji ke dauke dasu wajen yin magana a matsayin kwararrun sojoji ga shugaban ku kuma babu wanda zai hana ku yi mini magana; duk abinda kuka fada mini a nan, ba za a kama ku da laifi ba kuma dole ku fada mana gaskiya, ba karya ba, shaidu da misalai idan aka bukaci hakan."

Ya bada tabbacin cewa, “Wadannan al’amura sun kasance doke mu cigaba da magance su don tabbatar da cewa an tanadar muku kayan aiki, don baku damar gudanar da ayyukan ku”.

KU KARANTA KUMA: Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)

Yace Za’a maganta dukkan matsalolin da sojojin suka gabatar, inda ya basu tabbacin cewa babu kwamandan da zai hukunta su akan bayyana matsalolin da suka yi. An bukaci yan jarida su bar dakin ganawan kafin rundunan su soma gabatar da kalubalensu ga shugaban rundunar sojin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel