An saka wa El-Zakzaky guba, mu na da hujja - Mabiya Shi'a

An saka wa El-Zakzaky guba, mu na da hujja - Mabiya Shi'a

Mabiya kungiyar 'yan uwa Musulmi (IMN) da aka fi sani da 'Shi'a' sun yi zargin cewa an saka wa shugabansu guba kamar yadda suka ce sakamakon binciken asibiti da aka gudanar a jininsa ya nuna.

Masu biyayya ga El-Zakzaky sun ce sakamakon binciken da aka gudanar a asibiti ya nuna cewa akwai sinadaran 'lead' da 'cadmium' masu guba a cikin jininsa.

A taron manema labarai da suka kira a ranar Laraba, Mikail Yunus, shugaban wakilan kungiyar, ya ce lafiyar jikin El-Zakzaky na cigaba da tabarbarewa.

Ya bayyana akwai adadi mai yawa na sinadarai masu guba a cikin jininsa, wadanda ke cigaba da kassara lafiyarsa.

Yunus ya kara da cewa binciken da kwararrun likitocin waje suka gudanar a kan jinin El-Zakzaky ya nuna cewar yana bukatar kulawar gagga wa.

A cewarsa, wata tawagar kwararrun likitoci ta fitar da cikakken rahoto a kan dukkan matakan da ya kamata a dauka domin ceto lafiyar El-Zakzaky.

Ya ce sun aika kwafi na rahoton zuwa babbar kotun Kaduna da ke sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna ke yi da El-Zakzaky. Ya ce sun mika wa kotun rahoton a ranar 17 ga watan Yuni.

DUBA WANNAN: Sai na bawa mata ta cin hanci kafin ta amince da ni, a raba auren mu ko na kashe kai na - Miji ya koka a gaban

Ya bayyana cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa El-Zakzaky ya na da matsala a idonsa na bangaren dama, lamarin da ke barazanar makantar da shi.

Kazalika, ya bayyan cewa El-Zakzaky ya samu toshewar magudanar jini a daya daga cikin jijiyoyin zuciyarsa, lamarin da ya ce ya saka El-Zakzaky a cikin hatsarin kamu wa da ciwon zuciya.

Ya kara da cewa, yanzu haka idon El-Zakzaky na bangaren hagu tamkar babu ne, saboda ko kadan ba ya gani da shi saboda ya kamu wa da wani ciwo da ake kira 'Anophthalmia'.

"Abin bakin ciki ne a ce an barsu haka shi da matar sa, lafiyarsu na kara tabarbare wa. Saidai ko idan so ake su mutu a daure.

"Daga karshe mu na kara jaddada bukatar mu ta a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da Malamah Zeenah domin su fita kasar waje a duba lafiyarsu," a cewar Yunus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel