Soyayya da maza masu aure ta fi dadi fiye da soyayya da samari - Budurwa ta ba da dalilai

Soyayya da maza masu aure ta fi dadi fiye da soyayya da samari - Budurwa ta ba da dalilai

- Wata budurwa ta bada wasu dalilai dake nuna cewa soyayya da maza masu aure tafi dadi fiye da soyayya da samari

- Budurwar ta bayyana cewa mace tafi samun kwanciyar hankali da kulawa idan tana soyayya da namiji mai aure

- Inda ta bayyana cewa samarin yanzu dole suje su koyo soyayya a gurin masu aure domin an barsu a baya nesa ba kusa ba

Wani bidiyo yana ta yawo a shafukan sada zumunta, inda yake nuna wata budurwa 'yar Najeriya tana bayyana cewa ta fi son soyayya da maza masu aure da samari.

Budurwar wacce taki bayyana sunanta ta ce ta fadi hakan ne saboda maza masu aure sunfi iya soyayya da kuma kwantar da hankali fiye da samari wadanda basu taba yin aure ba.

A cewar budurwar samari suna bukatar su tsaya su koyi soyayya a wurin masu aure.

KU KARANTA: An kuma: Amarya ta yiwa mijinta allura da fiya-fiya jim kadan bayan bikinsu

Ga abinda budurwar ta rubuta:

"Maza masu aure sunfi dadin soyayya fiye da samari, saboda sun iya kalamai masu dadi kuma basu dorawa mace wahala da yawa.

"Idan kina soyayya da namiji mai aure, kin fi samun kwanciyar hankali, kuma suna da kulawa sosai.

"Samari dole suje su koyo soyayya a gurin masu aure, saboda gaskiya babu abinda suka sani akan soyayya.

"Amma idan kina auren mai aure zaki ga salon soyayya kala-kala da kulawa kamar zai cinye ki."

Yanzu dai lamarin soyayya tsakanin samari da 'yan mata ya zama sai du'a'i domin kowa yana soyayyar ne saboda wata bukata ta kanshi ba duka bane ke soyayyar domin Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel