Jerin kasashe biyar da rabin masu fama da matsanancin talauci a duniya ke rayuwa - Rahoto
- World Bank Poverty (WBP) ta lissafa jerin kasashe biyar da rabin mutanen duniya masu fama da matsanancin talauci ke rayuwa
- Kasashen India, Najeriya, Ethiopia, DRC da Bangladesh suna da kimanin mutanen da ke fama da matsanancin talauci miliyan 736
- A yayin da Bankin Duniya ke ganin alamun canji a India da Bangladesh, babu alamar samun canji a sauran kasahen uku
A ranar Talata, 18 ga watan Yuni ne aka bayyana cewa rabin mutane da ke fama da matsancin talauci a duniya miliyan 736 a 2015 suna rayuwa ne a kasashe biyar na duniya.
A cewar Kungiyar bincike na Bankin Duniya, 'World Bank Poverty' (WBP) wadandan kasahen biyar su ne India, Najeriya, Jamhuriyar Congo (DRC), Ethiopia da kuma Bangledesh.
DUBA WANNAN: Kotu ta dakatar da daya daga cikin masu ikirarin shugabancin majalisar Bauchi
WBP ta kuma kara da cewa wannan kasashen biyar su ne kasashe da suka fi yawan al'umma a Kudancin Asia da Nahiyar Afirka kuma wadannan yankunan ne ka da kashi 85 cikin 100 na mutane da ke fama da talauci a duniya.
Kungiyar ta Bankin Duniya ta ce akwai bukatar a bullo da hanyoyin rage talauci a duniya zuwa kasa da kashi 3 cikin 100 a shekarar 2030 ta hanyar fara magance talaucin a kasashen da ke fama da matsanancin talauci.
WBP tace akwai alamun cewa talaucin zai ragu sosai a kasashen India da Bangledesh a 2030 amma babu alamar afkuwar hakan a Najeriya, DRC da Ethiopia.
A baya, Legit.ng ta kawo muku wani rahoton na Bankin Duniya da ya ce Najeriya na cikin kasashen da tattalin arzikin su bai samu wata cigaba ba tsakanin 1995 zuwa 2018.
Hakan na cikin wani rahoto ne mai lakabin Africa's Pulse da aka fitar a ranar Litinin 8 ga watan Afrilun 2019 inda akayi fashin baki kan batutuwa da suka shafi Afirka.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng