Kunji ita kuma: Wallahi ba zan iya auren saurayin da ba zai saka mukullin mota a kayan aurena ba - In ji wata budurwa

Kunji ita kuma: Wallahi ba zan iya auren saurayin da ba zai saka mukullin mota a kayan aurena ba - In ji wata budurwa

- Wata budurwa ta yi wani abu wanda ya bai wa kowa mamaki

- Yayin da mazan aure suke wahala a wannan zamanin, sai gashi ita kuma taki yarda da bukatar aure da wani saurayinta yayi mata

- Inda ta bayyana mishi cewa dole sai ya siya mata mota koda za ta iya auren shi

A yanzu da maza suka zama tamkar zinare, kuma mata suke kara yawa, zai yi wuya mace ta ki amince da zancen aure. Saboda kusan kowacce budurwa a wannan lokacin abinda take jira kenan.

Sai dai hakan bai dami fitacciyar 'yar wasan fina-finai ta kudancin Najeriya ba, Olive Utalor, wacce taki amince da auren wani saurayi nata shekarun da suka gabata.

Olive ta yi hakan ne a cewar ta saboda saurayin nata bai sako mukullin mota a cikin kayan aurenta ba.

"Ranar bikin murnar ranar haihuwata yayi mini alkawarin mota, yanzu kuma ni yake so, bazan taba aurenshi babu mota ba. Ban damu ba duk da yayi dawainiya dani lokacin ina karatu. Bazan iya tafiya cikin rana ba bayan nayi aure. Yaje ya nemi daidai shi," hirar jarumar kenan da wata kawarta lokacin data nemi taji dalilin da yasa taki amincewa da auren.

KU KAARANTA: Dubu ta cika: Ina sayar da kan mutum namiji naira 170,000 kan mace kuma naira 160,000 - In ji Mustapha Aliyu

Rahotanni sun nuna cewa, saurayin yana aikin koyarwa a makarantar Firamare, a ranar bikin murnar ranar haihuwar shi yana tunanin cewa da yayi mata magana zata amince, ashe abin ba haka bane, saboda taki amincewa. Tsananin bakin ciki yasa yaje kan titi domin mota ta buge shi ya huta.

Duka lamarin ya faru a wani katon shagon sayar da kaya na garin Asaba, jihar Delta, kafin idon mutane ya dawo kan lamarin, saurayin yayi tunanin ya riga ya gama tsara komai, ashe ita ma budurwar tana da nata tsarin a zuciya.

"Bazan iya yaudarar kaina nace shine ya dace dani ba. Gaskiya ne ya ganni lokacin ina yarinya lokacin ina karatu, amma hakan ba yana nufin mun dace da juna bane. Idan har ba zai iya siyo mini mota ba, gaskiya bazan iya aurar shi ba," in ji ta.

Jarumar 'yar jihar Delta yanzu haka tauraruwar ta na haskawa a a cikin jaruman fina-finan, domin kuwa an sanyata a wasu fina-finai wadanda sunyi kasuwa sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel