Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal

Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal

Wani jirgin sama na kamfanin Air Peace ya ketare titin sa a filin tashi da saukan jirage na Fatakwal da ke jihar Rivers yayin da ake ruwan sama da bakin kwarya.

A cewar daya daga cikin fasinjan da ke jirgin, lamarin ya faru ne a yayin da jirgin ke sauka a filin saukan jiragen kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Jirgin ya yi birki a cikin daji kimanin mita 200 daga titin sa.

Wani shaidan ganin ido ya ce an fitar da dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin an koma da su wurin da ya dace jirgin ya tsaya tun farko.

Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal
Jirgin sama na Air Peace da ya kubce ya shiga daji yayin sauka a filin tashi da saukan jirage na Fatakwal
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: An kama kwararen mayaki na kasa da kasa cikin 'yan Boko Haram a Borno

Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal
Jirgin sama na Air Peace da ya kubce ya shiga cikin daji yayin sauka a filin saukan jirage na Fatakwal
Asali: Twitter

Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal
Fasinjojin jirgin Air Peace yayin da ake tallafa musu fitowa daga jirgin da ya shige daji a Fatakwal
Asali: Twitter

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164