Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu

Manyan mutane da yawa a duniya sun zamanto wasu ne ta sanadiyyar matayensu, kuma da yawa daga cikinsu suna yin alfahari da matayen nasu. Marigayi Obafemi Awolowo ya taba yin wata magana wacce ke nuna yabo da kodawa ga matarsa. Haka shi ma Bill Clinton, shugaban kasar Amurka na 42, shima ya taba koda matar tasa a lokacin da yake yakin neman zabe.

Hakan yana nuni da irin jin dadin zama da kuma taimaka musu da suke yi sau da yawa a harkoki na rayuwarsu. Sau da yawa idan namiji ya samu mulki ko sarauta, zaka tamkar matarsa ce ke gabatar da mulki.

Daga kan Maryam Ibrahim Babangida zuwa kan Aisha Buhari, mun yi kokari mun binciko muku yadda suka tafiyar da mulkinsu a matsayinsu na matan shugaban kasa.

Maryam Babangida (1985-1993)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Maryam Babangida
Asali: Facebook

Maryam Babangida ita ce matar tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (retd) wanda yayi mulki daga shekarar 1985 zuwa 1993.

Duk da cewa an haifeta a garin Asaba ne, Maryam ta kasance mai son mulki, inda kowa ya gane son mulkin nata a fili. Hakan ya samo asali lokacin da ta samu karin mukami a shekarar 1983, lokacin da mijinta ya zama shugaban hukumar soji a lokacin mulkin soji na shugaban kasa Muhammadu Buhari. Da wannan matsayi na mijin nata yasa take ganin kanta a matsayin matar babban hafsan soji na Najeriya.

A lokacin da mijinta ya yiwa maigidan nasa juyin mulki, Maryam ta kasa boye farin cikinta akan nasarar mijinta ya samu. Maryam ce ta fara samar da shirin da zai taimakawa matan karkara, domin fitar dasu daga matsanancin talauci.

Maryam ta ki bari mutane su san matan gwamnoni a wannan lokaci, saboda tana tsoron sunanta zai disashe a idon duniya idan mutane suka sansu. Ta bi kowacce hanya ta zama ita kadai ce mace da ta ke haskawa a lokacin mulkin mijinta.

Sannan tayi kokari ta hana a baiwa kowacce mace mukamin minista a lokacin mulkin mijin nata. Haka kuma ita ce ta hada tuggun cire Francesca Emmanuel, wacce take ita kadai ce take da mukamin darakta janar a ma'aikatun Najeriya.

Maryam Babangida ta rasu a ranar 27 ga watan Disamba, bayan ta sha fama da rashin lafiya na ciwon daji.

Maryam Abacha (1993-1998)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Maryam Abacha
Asali: Facebook

Lokacin da Maryam Abacha ta shiga ofishin uwargidan shugaban kasa, wanda ta karba daga hannun Maryam Babangida, maimakon abin yayi sauki, sai ta giyar mulki ita ma ta dauke ta, inda a lokacin ta sa aka bai wa babbar 'yarta Zainab, ofishin na 'yar gidan shugaban kasa.

Maryam Abacha ta dauki wannan matsayi da take dashi da mutukar muhimmanci. Misali ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da aikin yi da kwangila ga 'yan uwanta da abokan arziki. Tsananin ji da kai da karfin mulki yasa tayi wata magana a lokacin da take hira da BBC, inda ta ce, duk wani minista ko jakadun kasashen waje da suke neman wata alfarma a gurin mijinta su fara zuwa su ganta, domin za ta iya share musu hawaye. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito a ranar 4 ga watan Nuwamba, 1999.

Kowa yasan cewa babu jituwa tsakanin Maryam Babangida da Maryam Abacha, saboda haka abu na farko da Maryam Abacha ta fara yi shine ta ta kawar da sunan Maryam Babangida ta kowanne hali daga idon duniya.

Maryam Abacha ta yi mulki na tsawon shekaru biyar, mulkin nata yazo karshe a lokacin da mijinta ya rasu a ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1998.

Fati Abdulsalami Abubakar (1998-1999)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Fati Abubakar
Asali: Facebook

Bayan mutuwar Sani Abacha a shekarar 1998, Abdulsalami Abubakar yakarbi ragamar iko. Matarsa ta shiga ofishin uwargidan shugaban kasa. Sai dai kuma ita taki yarda tayi amfani da sunan 'First Lady'. Fati wacce take alkali ce a kotun koli ta yiwa ofishin uwargidan shugaban kasa kwaskwarima, inda a lokacinta ne aka samu sassauci saboda adalcin ta, domin ta ruguza duk wasu abubuwa da basu kamata da magabatanta suka yi.

Fati ce ta kafa kungiyar yancin mata da kuma basu kariya ta (WRAPA). Ta bi dukkanin hanyar da ta kamata wurin ganin ta tabbatar da wannan kungiya. An gano cewa Fati ce wacce ta tirsasa mijinta ya mika mulki ga zababben shugaban kasa da aka zaba a wannan lokacin.

Stella Obasanjo (1999-2005)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Stella Obasanjo
Asali: Facebook

Bayan shafe shekaru goma sha shida ana mulkin soja, Najeriya ta koma mulkin demokradiyya, lokacin da shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara gabatar da mulkin shi a matsayin zababben shugaban kasa. Ya fada kanshi cewa matar shi ba ta da wani matsayi da ya wuce matar shugaban kasa. Sai dai kuma, ya dauki stella Obasanjo watanni shida kawai, ta canjawa mijin nata ra'ayi, inda ya ya barta ta fara amfani da sunan 'First lady'. Stella ce ta fara dawo da tsarin Maryam guda biyu da aka yi a baya.

Ita ma ta zuba mulki a lokacin ta, a lokacin ta ne take fitowa kafar yada labarai ta yiwa al'ummar Najeriya magana a matsayin mijinta. Sai dai kuma ta samu cikas, inda ba ta samu damar gabatar da mulki kamar yadda sauran matan shugaban kasa na baya suka gabatar ba, saboda a lokacin mulkin dimokradiyya ne, kuma akwai matan mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar (Titi da Jamila) wadanda take gogayya da su.

A lokacin ne Titi Abubakar ta kirkiro wata kungiya da take hani ga masu safarar 'ya'ya mata. Kungiyar ta sa Titi ta fara suna a duniya. Hakan ya sa kishin Stella ya fito fili. Stella ta yanke hukuncin sanyawa Titi birki, inda ta nuna mata cewa ita matar mataimakin shugaban kasa ce.

A ranar 24 ga watan Yuni 2003, Stella ta kira dukkanin matan gwamnonin kasar nan, inda ta bayyana musu cewa matar shugaban kasa daya ce kawai a Najeriya. Sanna tayi musu hani da karbar matar mataimakin shugaban kasa a duk lokacin da ta kai musu ziyara jihohin su.

Stella Obasanjo ta mutu a ranar 23 ga watan Oktoba, 2005, a lokacin da ake yi mata canjin halitta da zai kara mata kyau a kasar Spain.

Turai Yar'Adua (2007-2010)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Turai 'Yar'adua
Asali: Facebook

Matar marigayi shugaban kasa Umaru Musa 'Yar'Adua halinta ya fito fili a lokacin da mijinta ya rasu. An bayyana cewa Turai ta yi iya bakin kokarinta wurin ganin an barta ta karasa shekarun mulki na mijinta, inda ta dinga hada kai da wasu manya a kasar nan domin ganin wannan buri nata ya cika.

Turai ta kafa cibiyar maganin ciwon daji a kasar nan. Mulkinta ya zo karshe ne a ranar 5 ga watan Mayu, na shekarar 2010, yayin da mijinta ya kwanta dama.

Patience Jonathan (2010-2015)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Patience Jonathan
Asali: Facebook

Idan an zargi sauran matan shugaban kasa da sun nuna kai da kuma son mulki, basu kai Patience Jonathan ba, wacce aka fi sani da Mama Peace. Ko kadan ba ta yi kama da matar shugaban kasa ba, saboda yanayin yadda take gabatar da abubuwan ta cikin nuna isa da kuma nuna halin ko in kula a irin abubuwan da take fada a matsayinta na matar shugaban kasa.

Mutane da yawa suna ganin ta taimaka wurin faduwar mijinta zabe a karo na biyu da yayi a shekarar 2015.

Bayan haka mutane da yawa baza su taba mantawa da ita ba, musamman ta bangaren yadda take yin magana cikin harshen turanci. Patience ta na yawan kwaba turanci a taruka da dama.

Aisha Buhari (2015 Zuwa yau)

Hotuna: Matayen shugabannin kasar Najeriya da aka yi daga 1985 zuwa yau, da dan takaitattun tarihinsu
Aisha Buhari
Asali: Facebook

Yayin da mijinta, Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce shi na kowane, sannan yasan matsayin da matarsa take dashi wurinsa, idan har ya taba cewa matarsa a wurin dafa abinci kawai take. Ta kowanne hali, Aisha kyakkyawa ce matuka wacce bata yi kama da masu shiga wurin dafa abinci ba.

Babu wani shugaban kasa a Najeriya da yake da mata da take kalubalantar mijinta kamar Aisha, tana tunani mai karfi, sannan tana tauna magana a duk lokacin da zata furta. Tana yawan kalubalantar mijinta a lokuta da dama.

Kwanan nan matar shugaban kasar ta bayyanawa 'yan Najeriya cewa daga yanzu a daina kiranta da sunan matar shugaban kasa, a dinga kiranta da sunan 'First Lady'

Yayin da mijinta ya fara gabatar da mulki a karo na biyu, mutane sun fara ganin halayenta a fili, ana ganin cewa zata kare kamar takwararta Aisha Hamani Diouri, matar tsohon shugaban kasar Nijar, Hamani Diouri, wacce ta zama babbar matsala a lokacin mulkin mijinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel