An tursasa wani dan shekara 14 auren budurwarsa yar shekara 15 bayan yayi mata ciki

An tursasa wani dan shekara 14 auren budurwarsa yar shekara 15 bayan yayi mata ciki

Inda ranka ka sha kallo, wani matashin yaro da wata matashiyar budurwa sun dauko ruwan dafa kansu bayan yan uwansu sun tursasa su auren junansu.

Tuni dai wani faifan bidiyon bikin aurensu ya yadu a yanar gizo, bidiyon yana nuna matashin da budurwar a lokacin da ake shirin daura musu aure.

A cikin bidiyon an gano amaryar dauke da juna biyu wanda ke nuna alamun cewa tana da ciki da wasu yan watanni.

Mahaifi amaryar wanda shima ya kasance a wajen bikin ya shawarce ta da yi a hankali yaayinda yake mika ta ga matashin angon nata, inda ya nusar da ita cewar a yanzu ba gaban iyayenta take ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Tuni dai bidiyon ya kawo cece-kuce a tsakanin masu amfani da shafukan sadarwa duba ga karancin shekarun yaran musamman ma mijin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda aka sace wasu 8 a sabon harin Zamfara

A halin da ake ciki, Legit.ng ta tattaro rahoto a baya wanda ke karin haske akan wasu dalilan da dake kai ga auren yara a Najeriya.

Rahoton ya daura hakan a kan talauci, al’adun gargajiya da rashin daidaituwa a banbancin jinsi a matsayin sauran dalilan dake kai ga auren wuri.

Auren wuri da kuma lalata har ila yau sun kasance daga cikin wahalhalun da matasa ke fuskanta idan aka yi musu auren dole.

Asali: Legit.ng

Online view pixel