Haka kawai: Wani mutumi ya budewa 'yan kilisar doki wuta a jihar Kano
- An cafke wani mutumi da ya budewa wasu mahaya doki wuta da bindiga jiya a jihar Kano
- Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya jiwa mutane bakwai raunika sakamakon harbin da yayi
- Yanzu haka dai mutumin na hannun hukumar 'yan sanda, za a mika shi zuwa kotu bayan an kammala bincike akan shi
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa matasa bakwai ne suka ji raunika sakamakon bude wuta da wani mutumi yayi ga wasu masu kilisar doki a Tudun Murtala dake jihar Kano jiya Laraba.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi, shine ya tabbatar da hakan yau Alhamis dinnan, ya ce mutumin wanda ya bude wuta ga mahaya dokin, Alhaji Idris Ali an damke shi, kuma za a gurfanar dashi a gaban kotu da an kammala bincike a kanshi.
KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Kano: Gwamna Ganduje ya yiwa al'ummar jihar wasu sabbin alkawura
Abdullahi ya ce: "Mun kwace bindigar mutumin, kuma bayan kammala bincike zam gurfanar dashi a gaban kotu, akan amfani da bindiga ba bisa ka'ida ba."
Kakakin hukumar ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ya umarci ayi kwakkwaran bincike akan lamarin, domin gano gaskiyar dalilin da yasa yayi harbin.
Ya ce har yanzu Ali yana hannun hukumar 'yan sandan, kuma baza su gajiya ba har sai sun gano gaskiyar lamarin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng