Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Gobara ta lashe rumfa 25 a babbar kasuwar Gombe

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Gobara ta lashe rumfa 25 a babbar kasuwar Gombe

- Gobara ta tashi a babbar kasuwar Gombe a safiyar ranar Laraba, 19 ga watan Yuni

- Lamarin wanda wutar lantarki ya haddasa yayi sanadiyar konewar rumfa 25

- Shugaban kungiyar yan kasuwar da ta kone, Alhaji Uba Abdullahi ya bayyana cewa kayayyaki na kimanin naira miliyan 50 suka kone

Ibtila’i ya afka ma babbar kasuwar Gombe, inda gobara ta lashe rumfa 25 a safiyar ranar Laraba, 19 ga watan Yuni.

Wani idon shaida ya bayyana cewa wutar ta fara ci tun da misali karfe 1:45 na tsakar dare sannan kuma ta shafe tsawon sa’o’i hudu tana ci, wanda hakan yayi sanadiyar konewar rumfa 25 kurmus.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai, Shugaban kungiyar yan kasuwar da ta kone, Alhaji Uba Abdullahi ya bayyana cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar, sannan kuma ya ce anyi asarar akalla dukiya kimanin naira miliyan 50 a gobarar.

Abdullahi ya kara da cewa wadanda ibtila’in ta cika da su sun hada da teloli, masu sana’ar kayan robobi, masu cinikin fata da dai sauransu. Ya kuma yi kira gay an kasuwar da su lazumci kashe kaya wuta kafin su tashi daga kasuwar don gudun sake afkuwar al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta bawa Sanusi da Ganduje sabon umarni a kan rikicin da suke yi

Sakataran ma’aikatar kasuwanci, Alhaji Muhammad Malala wanda ya ziyarci kasuwar ya jajantawa wadanda lamarin ya ritsa da su sannan ya yi alkawarin sanar da gwamnati kukan su don daukar matakin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel