Wani matashi da ya kashe kanshi ya bar wa iyayenshi wasika mai ratsa zuciya

Wani matashi da ya kashe kanshi ya bar wa iyayenshi wasika mai ratsa zuciya

- Wani matashi dan bautar kasa ya kashe kanshi a Ibadan

- Matashin ya rubuta wata wasika ya barwa iyayenshi akan dalilin da yasa ya kashe kanshi

- Ya kuma roki gafarar iyayenshi akan irin wahalar da suka sha dashi wurin ganin ya samu yayi karatu

Wani dan bautar kasa Mista Johnson Onyilo, wanda ya kashe kanshi a garin Ibadan, ya bar wata takarda wacce ke dauke da dalilin da ya sa ya kashe kanshi, sannan kuma ya roki iyayenshi akan su yafe mishi.

Onyilo, yana bautar kasa a karamar hukumar Ibadan ta gabas maso yamma, kafin lamarin ya faru.

Daga baya an gano marigayin wanda yayi karatun fannin banki a jami'ar Jos dake jihar Filato, yana zaune da 'yar uwarshi ne lokacin da yake bautar kasar.

KU KARANTA: Kwamishinan 'yan sanda: Yadda makiyaya ke amfani da dabbobi suna boye bindigogi

Da yake hira da jaridar Vanguard, jami'ar hulda da jama'a ta 'yan bautar kasa na jihar, Mrs. Christy Olatoye, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta yi addu'ar Allah ya kare matasa daga aikata irin wannan aikin dana sani.

Za a dauki gawar marigayin a kai jihar Binuwai domin binne shi bisa yadda addininsu ya tsara.

Da wakilin Vanguard ya kira jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, SP Gbenga Fadeyi, ya bayyana cewa har yanzu ba a kawo mishi rahoto akan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel