NNPC za ta cigaba da neman mai a arewa

NNPC za ta cigaba da neman mai a arewa

-Hukumar NNPC ta ce zata cigaba da neman danyen man fetur a yankin Chadi

-Shugaban hukumar Dr. Maikanti Baru ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Bauchi

-Baru ya ce sun dakatar da binciken ne sakamako harin da yan Boko haram suka kaima ma'aikatansu, kuma da zarar sun samu tabbacin tsaro daga hukumomin tsaro zasu koma bakin aiki.

Hukumar samar da albarkatun man fetur ta kasa (NNPC) ta ce zata ta cigaba da binciken dayan man fetur a yankin Chadi da zarar ta samu tabbacin tsaro daga hukumomin tsaro.

Babban daraktan hukumar, Dr. Maikanti Baru ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke karbar gwamnan jihar Bauch a ranar Laraba 19 ga watan Yuni 2019.

Ya tabbatar da cewa akwai yiyuwar a gano danyan man fetur a yankin na Chadi.

Ya ce “Zamu koma da zarar muka samu tabbaci daga hukumomin tsaro. Akwai yiyuwar a samu mai a wajen saboda jamhuriyar Nijar ta hako rijiyoyin mai guda 600 kuma yanzu suna fitar da man, mu kuma mun hako rijijyoyi 23 ne kawai.”

Baru ya yabawa mutanen garin Bauchi da Gombe musamman mutanen da ake aikin hako man a garuruwansu. Ya kuma bada tabbacin cewa hukumar ta NNPC zata taimaka masu da kayan more rayuwa.

Ya kuma yi alkawarin cewa zasu gina makarantar karatun albarkatun man fetur a cikin jami’ar jihar Bauchi.

Ya kuma bawa gwamnan tabbacin hadin kai tsakanin makarantar albarkatun man fetur dake a Warri da kuma wadda za a gina a Bauchi.

KARANA WANNAN: APC ba da gaske su ke yi ba kuma IBB ne Ummul Haba’isin Kasar nan –Falana

Shugaban hukumar ta NNPC, ya ce sun dakatar da binciken danyan man futur bayan da yan boko haram suka kaima masu binciken hari a cikin watan Yuli 2017 a inda har akayi garkuwa da wasu daga cikinsu.

A lokacin da yake maida jawabi, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed ya ce ziyarar na da zummar yin hadaka tsakanin hukumar ta NNPC da kuma jihar Bauchi don ganin yadda za a ciyar da jihar gaba.

Ya kuma bayyana cewa a shirye suke da su bada gudunmuwa wajen binciken da NNPC takeyi a yankin nasu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng