Umara Zulum ya nada mukarrabai a Gwamnatin Jihar Borno
Labari ya zo gare mu cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar da wasu sababbin nadin mukamai a Ranar Laraba 19 ga Watan Yunin 2019 bayan ya yi makonni 3 a ofis.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya nada Alhaji Jidda Usman Shuwa a matsayin Sakataren gwamnatin jihar watau SSG. Isa Umar Gusau zai cigaba da rike kujerar da ya ke kai a halin yanzu.
Isa Gusau shi ne zai rika taimakawa gwamnan wajen sha’anin hulda da ‘yan jarida da kuma dabarun yada labarai. Mun samu duk wannan rahoto ne daga jaridar nan ta Yerwa Express News.
Babangana Wakili shi ne zai zama shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin na jihar Borno. Haka zalika gwamna Zulum ya nada Barista Mustapha Ali Busuguma a matsayin babban Sakatarensa.
KU KARANTA: Dalilin da ya sa na zauna da Shugaba Buhari Inji Zulum
Sauran mukaman da gwamnan ya bada sun hada da mai bada shawara a kan harkokin waje inda ya nada Ambasada Adamu Abbas. Baba Sheikh Haruna ya zama Hadimin gwamnan na labarai.
Shi kuma Alhaji Ahmed Sanda zai taimakawa gwamnan wajen harkar tsare-tsare da gudanarwa. Sanarwar ta ce Dr. Mairo Mandara za ta taimaka wajen jagorantar aikace-aikacen SDG a Borno.
Malam Tahiru A. Tahir da Abdulrahman Ahmed Bundi su na cikin wadanda za su rika ba gwamna shawara a kan harkar yada labarai. Ahmed Bundi zai rika aiki ne da sauran kafefen zamani.
Dazu kun ji cewa shugaban kasa Buharii ya samu lokaci ya zauna da sabon gwamnan jihar Babagana Zulum na cikin fadar Aso Villa a lokacin da ya tattauna da gwamnonin jihohin kasar.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng