Mata sun yi zanga-zanga akan hare-hare da kashe-kashen yan bindiga a Taraba

Mata sun yi zanga-zanga akan hare-hare da kashe-kashen yan bindiga a Taraba

- Mata a Taraba sun gudanar da wani zanga-zanga akan hare-haren da aka kai jihar

- Matan sun koka kan kisan mazaje da yaransu

- Masu zanga-zangan sun kuma yi zargin cewa sojoji sn hana su sannan suka jima wasu rauni

Matan kauyen Kona da ke karamar hukumar Jalingo na jihar Taraba a ranar Talata, 18 ga watan Yuni sunyi zanga zanga akan hare-hare da kashe-kashen da yan bindiga suka yi kwanan nan a kauyensu.

Matan wadanda ke zanga zanga kan mutuwar mazajensu da yara a hare-haren sun mamaye titunan Kona Garu a Jalingo suka kuma kare a ATC.

Sun yi korafin cewa sun razana da harin da ake cigaba da daukakawa kamar yanda yan bindigan suka kai mamaya kauyukan kan babura inda suka yi harbe-harbe da kone-konen gidaje.

Har ila yau sun bukaci a saki matasansu cikin gaggawa wanda suke ikirarin yan sanda sun kama. Matan har ila yau sunyi zargin cewa Rundunan Soji ta katse zanga-zangan sannan suka ji ma wasu daga cikin su rauni.

Babban kwamandan bataliya na 20 Model, Serti, Laftanal Kanal Mohammed Adamu a hiran wayar talho, ya musanta zargin cewa mutanensa suna da hannu cikin zanga-zangan matan.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, David Misal yace an samar da isasshen tsaro ga mata masu zanga zangan a lokacin da suka gudanar da zanga-zanga a tituna. Ya kara da cewa a halin yanzu an samar da zaman lafiya a kauyukan da lamarin ya shafa.

Har ila yau ya tabbatar da kamun wasu matasa wadanda suka mallaki makamai masu hatsari, inda ya kara da cewa a halin yanzu ana kan gudanar da bincike.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta na bada agajin abubuwan more rayuwa saboda sakacin Gwamnati - Rabaren Manoso

Mutanen kauyen sunyi ikirarin cewa an kashe akalla mutane takwas a hare-haren da ya shafi kauyuka a Kona da ATC wanda aka fara daga daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita daga safe zuwa dare a yankunan da lamarin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: