Kotu ta bayar da umurnin tsare mutumin da ya bayar da shaidan zur kan Gwamna Ishaku

Kotu ta bayar da umurnin tsare mutumin da ya bayar da shaidan zur kan Gwamna Ishaku

Kotu ta bayar da umurnin kama tsare wani jami'in gidan yari, Usman Ajuji bisa zarginsa ba bayar da shaidan zur ga kwamitin bincike ta musamman na fadar shugaban kasa Special Presidential Investigation Panel (SPIP).

Ana zargin Ajuji, ma'aikacin Hukumar Kula da Gidajen Yari reshen jihar Yobe da laifin bayar da bayannan karya kan Gwamna Darius Ishaku na jihar Yobe.

Dan sanda mai shigar da kara, Celestin Okpong ya shaidawa kotun Majistare da ke Wuse Zone 6 a Abuja cewa 'mai tonon asirin' ya bayar da bayannan karya ga shugaban SPIP, Okoi Obono-Obla a ranar 7 ga watan Yuni cewa yana ta tabbas akwai jakunkunan kudade a gidan gwamnan Taraba da ke Wuse Zone 1.

DUBA WANNAN: Kasashen Afirka 7 da 'yan Najeriya za su iya ziyarta ba tare da biza ba

Sai dai an kai sumame gidan amma jami'an SPIP ba su ga kudin a gidan ba. Hakan ya sabawa sashi na 140 na dokar Penal code.

Sai dai wanda ake tuhumar bai amsa lafin da ake zarginsa a aikatawa ba.

Hakan ya sa, alkalin kotun, Majistare Ahmed Indajiwo ya bayar da belin wanda ake zargin kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su karbe shi belin.

Ya bayar da umurnin a bawa wanda ake zargin masauki a gidan yarin Keffi kafin ya cika ka'idojin belinsa.

Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164