Allah wadan naka ya lalace: Wata mata ta tona asirin aminin mijinta da ya bukaci yin zina da ita
- Wata mata ta bayyana yadda aminin mijinta ya bukaci ya kwanta da ita, bayan maigidanta yayi tafiya
- Matar ta ki amincewada bukatar abokin mijin nata bayan wata hira da suka yi da shi a WhatsApp
- Daga baya da yaga cewar babu nasara a wurin matar mutumin ya nuna mata cewa wasa yake yi mata
Asirin wani mutumi mai suna Mista Bayo ya tonu, yayin da aka sanya wata hira da yayi da matar babban abokinsa a shafin sada zumunta na Twitter.
A cikin hirar ta su da aka sanya a Twitter din, mutumin wanda aka bayyana sunansa da Bayo ya bukaci matar aminin nasa da ta bashi dama yazo gidanta ya taya ta kwana.
KU KARANTA: Masarautar Rano: Hakimai 4 sun yi kunnen uwar shegu da umarnin da Sarki ya basu
Matar wacce alamu suka nuna cewa tana zaune da mijinta cikin amana, ta bayyanawa Bayo cewa ta na zaune lafiya ita da 'ya'yanta, kuma bata bukatar zuwan shi, inda kuma ta bayyana cewa bata ji dadin irin wannan maganar ta na fitowa daga bakinsa ba.
Bayan yaga cewa matar aminin nasa baza ta bashi hadin kai ba, Bayo sai ya wayance da cewa dama yana gwada ta ne domin yaga tana cutar mijinta ko bata yi, kuma sai gashi ta cinye jarrabawar. Sannan kuma ya sanar da ita cewa kada ta sake ta gayawa mijinta hirar da suka yi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng