Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe yan achaba 2 a Kaduna
- Masu fashi da makami sun kashe yan achaba guda biyu a wani gidan mai ke Kaduna, a tsakar daren jiya Lahadi
- Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:45 na tsakar dare lokacin da yan fashin suka kai mamaya gidan man inda a nan ne yan achaba ke kwana
- Yan fashin sun kuma tafi da babur din daya daga cikin wadanda suka kashe
Wasu da ake zargin yan fashi da makami ne sun kashe yan achaba guda biyu a wani gidan mai ke Kaduna, a tsakar daren jiya Lahadi, 16 ga watan Yuni.
Maharan sun yiwa yan achaban kisan wulakanci a gidan man Usmania da ke a hanyar babban titin Nnamdi Azikwe, Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:45 na tsakar dare lokacin da yan fashin suka kai mamaya gidan man inda a nan ne yan achaba ke kwana.
Yan fashin sun yi masu fashin wayoyi da kudade kafin su kashe su.
Daya daga cikin mutanen, wanda ya tsira da ransa a harin, Rayyanu Yahaya Dawakin Tofa, yace yan fashin sun sace masa wayoyi da kudade.
“Duk muna bacci a lokacin da suka zo gidan man dauke muggan makamai kamar su wukake da bindigogi.
“Sun bukaci mu basu wayoyinmu da kudade wanda na aikata ba tare da na furta komai ba. Daya daga cikinsu ya mare ni a fuska sannan ya bukaci na kwanta a kasa.
“Sun kuma aikata hakan ga wasu yan achaba biyu da ke ikinmu. An harbi daya daga cikinsu saboda yayi yunkurin guduwa yayinda aka soki dayan har lahira kan yayi ihu,” inji shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan fashin sun kuma tafi da babur din daya daga cikin wadanda suka kashe.
KU KARANTA KUMA: Majalisar zartarwa: Buhari zai tuntubi shugabannin APC na kasa da jiha
Mammalakin gidan man, Alhaji Abubakar Usman Sharif yace an sanar da lamarin ga hukumar tsaro.
Da aka tuntube shi, kaakakin yan sandan jihar, DSP Yaakubu Sabo, wanda ke a cikin wata ganawa yace za a ji daga gare shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng