Waiwaye: Gaskiyar abinda yasa Buhari ya rabu da matarsa ta farko, Safinatu
Kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya auri Aisha, ya auri wata matar mai suna, Safinatu, wacce suka haifi 'ya'ya biyar; hudu mata, daya na miji, a cikin shekaru 17 da suka yi tare.
Safinatu diya ce ga Alhaji Yusuf Mani, tsatson Shehu Usma Danfodiyo, da Hajiya Hadizatu Mani. An haife ta a ranar 11 ga watan Disamba na shekarar 1952 a garin Jos, wacce yanzu ke zaman babban birnin jihar Filato.
Iyayen ta 'yan asalin karamar hukumar Mani ne da ke jihar Katsina.
Buhari ya hadu da Safinatu ne a lokacin yana manjo a rundunar soji a shekarar 1966 lokacin tana da shekara 14 a duniya. Sun hadu ne a Legas lokacin da Buhari da marigayi Shehu Musa Yar'adua suka ziyarci gidan mahaifin Safinatu lokacin yana aiki a Legas a matsayin sakatare ga mahaifin Yar'adua, wanda a lokacin shine ministan harkokin Legas.
Buhari ya auri Safinatuu a shekarar 1971 bayan yakin basasa ya kare. Safinatu ce matar Buhari a lokacin da ya mulki Najeriya a mulkin soji. Sun haifi 'ya'ya biyar; Zulaihat, Fatima, Musa, Hadiza da Safinatu. Musa ya mutu tun yana karami, yayin da Zulaihat ta mutu a shekarar 2012.
Al'amura sun canja a rayuwarsu ta aure bayan Babangida ya jagoranci hambarar da gwamnatin Buhari a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1985, sannan kuma ya garkame shi na tsawon shekaru uku.
Daya daga cikin abubuwan da Buhari ya yi bayan fitowarsa daga gidan yari shine sakin Safinatu.
DUBA WANNAN: Matar gwamnanan APC ta zama shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa
Duk da dalilin rabuwar auren ba daga bakin Buhari ya fito ba, majiya mai karfi ta bayyana cewar Buhari ya saki Safinatu saboda mu'amalar ta da gwamnatin Babangida, musamman kawancen ta da Maryam Babangida.
Jaridar 'City People' ta rawaito cewa Safinatu ta bayyana cewar ta kulla alaka tare da kusantar gwamnatin Babangida ne ko hakan zai sa a sako mijinta, sannan kuma rayuwa ta fara yi musu wahala saboda garkame Buhari da Babangida ya yi.
City People ta ce Buhari ya gargadi Safinatu cewar kar ta sake ta sakar wa Babangida fuska balle ta kusanci iyalinsa ko gwamnatinsa bayan sun yi masa juyin mulki.
Shekara daya bayan rabuwar aurensa da Safinatu, Buhari ya auri Aisha lokacin tana da shekaru 18 a duniya.
Safinatu ta mutu a ranar 14 ga watan Janairu na shekarar 2006 bayan ta sha fama da ciwon sukari. An binne ta a makabartar Unguwar Rimi a garin Kaduna.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng