Kunji fah: Gwaggon biri ya sace naira miliyan 10 a gidan Zoo din Kano

Kunji fah: Gwaggon biri ya sace naira miliyan 10 a gidan Zoo din Kano

- Ana zargin gwaggon biri da sace naira miliyan goma a gidan Zoo din jihar Kano

- A jiya ne aka bada sanarwar bacewar kudin a gidan Zoo din

- Rahotanni sun nuna cewa kudin cinikin da aka yi ne a wannan bukukuwan karamar sallar

A jiya ne muka kawo muku rahoton cewa an nemi cinikin bukukuwan sallah da aka yi a gidan Zoo na jihar Kano an rasa.

A cikin daren jiyan ne gidan Rediyon Freedom na jihar Kano ya cigaba da gabatar da bincike akan yadda aka yi miliyan goma na cinikin gidan Zoo din ta yi batan dabo.

Wasu jami'an gidan Zoo din sun bayyana cewa suna zargin wani Gwaggon biri da sace miliyoyin kudaden, kuma har yanzu ba a san inda ya boye kudin ba. Sai dai kuma sun bayyana cewa suna zargin da ya sace kudin hadiyewa yayi.

KU KARANTA: Tirkashi: Barayi sun sace cinikin Sallar da aka yi a gidan Zoo na Kano

Wakiliyar gidan Rediyon Freedom din da ta ziyarci gidan Zoo din da ranar yau, ta samu dukkanin jami'an gidan Zoo din a kulle, sai kawai masu sayar da tikiti wadanda suke a bakin gate, da kuma baki wadanda suke shigowa kallon dabbobi.

Sai dai kuma wadansu ma'aikatan gidan Zoo din, sun bayyanawa wakiliyar gidan rediyon cewa zancen batan kudi a daina dorawa gwaggon biri, saboda bai san komai akan maganar ba, kuma bashi da hannu a cikin batan kudin.

Sun kara da cewa akwai wasu mutane masu kama da birrai, wadanda suka shigo suka sace kudin. Suka ce daga yaya za ayi ace biri ya bude kejin da yake ciki a kulle ya je ya sace kudi?

Wakiliyar gidan rediyon ta je inda kejin gwaggon birin yake, inda ta tarar 'yan kallo sun kewaye shi suna kallo a matsayin barawo, shi kuwa gwaggon birin ya tsaya yana kallonsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel