Jerin sunaye: Shugabanin kasashen Afirka 11 da suka hallarci bikin ranar demokradiyyar Najeriya

Jerin sunaye: Shugabanin kasashen Afirka 11 da suka hallarci bikin ranar demokradiyyar Najeriya

A kalla shiugabanin kasashen Afirka 11 ne suka hallarci taron bikin sabuwar ranar demokradiyyar Najeriya a ranar Laraba 12 ga watan Yunin 2019.

Shugabanin da suka hallarci taron sun hada da Idris Deby na kasar Chadi; Shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz na Mauritania; Shugaba Paul Kagame na Rwanda, Shugaba George Weah na Liberia; Shugaba Denis Sassou Nguesso na Congo da Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana.

Sauran sun hada da Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe; Shugaba Macky Sall na Senegal; Shugaba Adama Barrow na Gambia da Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar da kuma Farai Ministan Uganda, Ruhakana Rugunda..

DUBA WANNAN: Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

Da isar sa farfajiyar Eagle Square da ke Abuja, Shugaba Muhammadu Buhari ya zagawa ya gaisa da dukkan shugabanin kasashen da wakilan wasu kasashen duniya da suka hallarci bikin.

Shugaba Buhari ya iso wurin taron misalin karfe 10.05 na safe, ya kalli pareti da Dakarun Sojojin Najeriya da Rundunar 'Yan sandan Najeriya su kayi sannan aka zaga da shi filin taron cikin motarsa.

Sauran manyan baki da suka hallarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa, Dolapo, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Femi Gbajabiamila.

Gwamnatin Tarayya ta yi bikin ranar Demokradiyya karo na farko ne a ranar 12 ga watan Yuni bayan shugaban kasa ya rattaba hannu kan dokar canja ranar demokradiyyar saboda zaben Yunin 1993 da a kayi ittifakin shine zabi mafi tsafta a tarihin Najeriya.

Cif MKO Abiola na jam'iyyar SDP ne ya lashe zaben inda ya doke abokin karawarsa, Bashir Tofa na jam'iyyar NRC amma tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Babangida ya soke zaben

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel