Za mu cigaba kamar yadda China da India suka cigaba – Shugaba Buhari

Za mu cigaba kamar yadda China da India suka cigaba – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kasar Najeriya tana da dukkanin abubuwan da ake bukata don samun cigaba kamar yadda kasashen China, India da Indonesia suka samu.

Buhari ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a bikin sabuwar ranar Dimukradiyya ta Najeriya, wanda ya dauke ranar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni sadaukarwa ga marigayi Cif MKO Abiola da ake ganin shine ya lashe zaben shugaban kasa na 12 ga watan Yunin 1993.

KU KARANTA: Waiwaye adon tafiya: Muhimman batutuwa 19 game da zaben ‘June 12 1993’

“Tun da har kasar China da India da Indonesia suka samu cigaba, toh banga abinda zai hana Najeriya samun cigaban da take bukata ba, China da Indonesia sun samu cigaba ne a karkashin tsarin mulkin kama karya.

“Yayin da Indiya ta samu cigaba a tsarin Dimukradiyya, da wannan nake ganin babu abinda zai hana Najeriya samun cigaba ita ma.” Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito Buhari yana fada.

Daga cikin karramawar da shugaba Buhari yayi ma Cif MKO Abiola akwai bashi lambar yabo ta GCFR, sauya ranar Dimukradiyya, da kuma canza sunan filin wasan Najeriya dake Abuja zuwa sunan MKO Abiola Stadium.

Daga karshe shugaba Buhari ya tabbatar ma mahalarta taron bikin ranar Dimukradiyyan daya gudana a dandan Eagle Square cewa zai mayar da hankali wajen cigaba da ayyukan cigaba daya fara da tabbatar da hadin kai a tsakanin yan Najeriya.

Sauran sun hada da iganta harkar kiwon lafiya, bayar da tallafi ga kananan yan kasuwa, dauke yan Najeriya daga kangin talauci, gina sabbin kananan hanyoyi da kammala manyan hanyoyi da suka kai tsawon kilomita 2000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel