Abin da mamaki: Wani mai kudi ya saci kaza don ya sayar ya sayi man da zai sanyawa motar da ya saya naira miliyan 140

Abin da mamaki: Wani mai kudi ya saci kaza don ya sayar ya sayi man da zai sanyawa motar da ya saya naira miliyan 140

- Wani abin mamaki da ya faru a kasar China, yayin da 'yan sanda suka kama wani mai kudi yana satar kajin mutane

- Mutumin babban manomi ne, ya samu karayar arziki

- Mutumin ya ce yana satar kajin ne saboda ya samu kudin da zai dinga sanyawa motar da ya saya naira miliyan 140 mai, saboda karayar arziki ta zo masa

An kama wani manomi mai arzikin gaske a yankin Sinchuan na kasar China, da laifin satar kaji da agwagi a wasu kauyuka da suke makwabtaka da garinsu, domin ya sayi man fetur da zai sanyawa wata mota kirar kamfanin BMW da ya saya akan kudi naira miliyan dari da arba'in (N140m).

Jami'an 'yan sanda a yankin Linshui suna ta samun korafi akan satar kaji da agwagi da ake yi a wasu kauyuka na yankin tun cikin watan Afrilu, amma basu ta ba kawowa wanda yake satar zai zamo daya daga cikin masu arzikin yankin ba, mutumin da yake zaune a gidan da babu irinsa a yankin, kuma yake tuka mota da tsadarta ya kai naira miliyan dari da arba'in.

Sai dai kuma, ashe karayar arziki ce ta sanya mai arzikin fadawa wannan harka ta sata, ya tsinci kanshi cikin halin kaka na kayi, bayan ya lura cewa ba zai iya sayen man fetur din da zai dinga sanyawa motarsa ba. Hakan ya tilasta shi fara satar kajin da agwagin mutane, yana kiwata su a gonarsa, sannan yana sayarwa yana sayen man fetur na motarsa.

KU KARANTA: Allah ya kiyaye gaba: An kone kasuwa yayin wani rikici da ya ritsa da Hausawa a jihar Osun

Bayan sun karbi korafi masu yawan gaske akan sace-sacen, sai jami'an 'yan sandan suka fara gabatar da kwakkwaran bincike, daga baya suka gano wani mutumi da yake zuwa akan babur wanda babu lamba. Sai suka dinga binshi har ya kai su gidan gonar mai arzikin.

Daga baya dai jami'an 'yan sandan sun gano cewa mutumin na kan machine din ba shine mai satar kajin ba, shima yana zuwa gidan gonar ne domin ya sayi kajin.

A karshe dai 'yan sandan sun gano cewa mai arzikin shine yake satar kajin, inda suka yi kokarin kamo shi domin yi masa tambayoyi, sai yayi amfani da motarsa ya gudu, suka kasa kama shi saboda motarsa tafi tasu gudu.

Bayan 'yan kwanaki 'yan sandan sun samu nasarar kama shi, inda kuma ya amsa laifinsa. Sannan ya bayyana dalilinsa na yin sace-sacen.

An kulle Qiang, bayan an yanke masa hukuncin sata. Labarinsa ya jawo hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta na zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel