Rayuwa bayan mutuwa: Wata budurwa ta bayyana yadda ta dawo duniya bayan kwanaki da mutuwar ta

Rayuwa bayan mutuwa: Wata budurwa ta bayyana yadda ta dawo duniya bayan kwanaki da mutuwar ta

- Wani labari mai ban mamaki da yake yawo a shafukan sadaa zumunta ya nuna yadda wata budurwa ta dawo duniya kwanaki kadan bayan mutuwar ta

- Matar tayi alkawarin bayyana irin abubuwan da ta gano a lahira

- Sannan ta bayyana cewa lahira babu dadi ko kadan

Labarin wata mata 'yar Najeriya na ta yawo a shafukan yada zumunta na zamani, bayan da ta bayyana cewa ta mutu sannan kuma ta dawo duniya bayan wasu kwanaki.

Mhiz Gold Abi, 'yar Najeriya ce da take zaune a Casablanca, birnin kasar Morocco, an bayar da rahoton cewa ta mutu, inda abokanan ta suka yi ta mamakin labarin. Wasu daga cikinsu sunyi ta jajen mutuwarta a shafukan sada zumunta. Bayan wasu 'yan kwanaki kuma sai ta hau shafinta na sada zumunta na Facebook ta bayyana cewa ta dawo duniya.

KU KARANTA: Kudin Paris Club: Yawan kudin da kowacce jiha ta samu a Najeriya

A matsayin ta na wacce ta mutu ta dawo, wacce ta ga lahira, ta bayyanawa abokanan ta na Facebook cewa lahira babu dadi ko kadan, inda ta rubuta cikin harshen turanci kamar haka "Heaven no easy oo."

Sannan tayi alkawarin bayyana irin abubuwan da ta gano a lahira, da irin abubuwan da suka faru da ita lokacin da take lahira.

Abokanan ta wadanda suka maida mata martani a labarin da ta rubuta din, sun bayyana jin dadinsu da ta dawo, sannan kuma sun yiwa Allah godiya da ya bata dama a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel