Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan dakarun Kamaru a gabar tafkin Chadi

Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan dakarun Kamaru a gabar tafkin Chadi

Dakarun sojoji uku na kasar Kamaru da mutane da dama sun riga mu gidan gaskiya a yayin aukuwar wani mummunan harin dare na 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hukumomin tsaro a ranar Litinin da ta gabata sun bayyana cewa, kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram sun yiwa wani sansanin dakarun soji diban karan mahaukaciya babu zato babu tsammani a gabar tafkin Chadi.

Wannan hari da ya auku a sansanin dakarun soji dak kauyen Darak a Yammacin tafkin Chadi cikin kasar Kamaru, ya salwantar da rayukan dakarun soji uku da kuma farar hula da dama da ba a san adadin su ba.

Tun kimanin tsawon shekaru goma da daurar damarar ta'addanci, kungiyar Boko Haram ta samwantar da rayukan kimanin mutane 27,000 tare da raba kimanin mutane miliyan 1.7 da mahallansu a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kawowa yanzu dakarun sojoji na kasar Najeriya, Chadi, Kamaru da kuma Nijar, sun gaza fatattakar wannan miyagun 'yan ta'adda da suka zamto alakakai wajen ci gaba da cin karen su babu babbaka musamman a gabar tafkin Chadi.

KARANTA KUMA: 'Yan majalisa 6 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Imo

Ana iya tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobi kan cewa sabuwar gwamnatin sa a wa'adin ta na biyu, ba za ta rangwanta wa dukkanin wasu 'yan ta'adda masu tayar da zaune a kasar nan.

Shugaban kasa Buhari yayin halartar taron kungiyar kasashen yankin tafkin Chadi da aka gudanar makonni biyu da suka gabata, ya ce lokaci ya karato da ya kamata a gaggauta kawo karshen ta'addancin Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel