An nada wasu Alkalai a Kotun Koli bayan tsohon CJN yayi murabus

An nada wasu Alkalai a Kotun Koli bayan tsohon CJN yayi murabus

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada wasu sababbin Alkalai a kotun kolin kasar. Mun samu wannan labari ne a Ranar Lahadi 9 ga Watan Yuni, 2019, daga bakin Malam Garba Shehu.

Garba Shehu wanda ya kasance mai magana da yawun bakin shugaban kasar, shi ya tabbatar da cewa shugaba Buhari ya nada wasu sababbin Alkalai a babban kotun Najeriya da ke Garin Abuja.

Shugaban kasar ya aikawa Alkalin Alkalan Najeriya na rikon kwarya takarda, inda yake sanar da shi game da wannan mataki da ya dauka. Hakan na nufin Alkalan kotun kolin sun kara yawa yanzu.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya dauki wannan mataki na kara yawan Alkalan da ke kotun koli ne kamar yadda sashe na 230 na tsarin mulki ya ba sa cikakken iko.

KU KARANTA: Buhari na iya mikawa Kabilar Ibo mulkin Najeriya a 2023

Malam Shehu wanda tun 2015 yake magana a madadin shugaban kasar ya ke cewa yanzu akwai Alkalai 21 a teburin babban kotun kasar, wanda wannan shi ne asalin abin da dokar Najeriya tayi tanadi.

Mai magana da yawun bakin shugaba Buhari ya kara da cewa wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta dauka yana cikin kokarin da ta ke yi na ganin shari’a na tafiya ba tare da kakkautawa ba.

Sai dai fadar shugaban kasar ba ta bayyana sunayen wadannan Alkalai da ta nada zuwa kotun kolin ba. A daidai wannan lokaci kuma shugaban kasar ya amince da murabus din tsohon CJN, Walter Onnoghen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel