Ango da Amarya sun rataya carbin takardar Naira da Dala a wurin bikinsu

Ango da Amarya sun rataya carbin takardar Naira da Dala a wurin bikinsu

- Wani Ango da Amarya 'yan Najeriya sun girgiza jama'a bayan yi carbin takardun kudi

- Ango da Amaryar sun rataya carbin takardun Nairori da Dalolin kasar Amurka a wuyansu

- 'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu a kan hoton Ango da Amaryar dake yawo a dandalin sada zumunta

Wani salon kwalliya da wani Ango da Amaryarsa suka yi amfani da shi yayin bikinsu ya saka 'yan Najeriya daga girar idanu tare da nuna mamakinsu a kan abinda sabbin ma'aurata suka yi don nuna farincikin ranar bikinsu.

Sabanin yin amfani da kayan kwalliya, ma'auratan sun zabi su yi amfani da takardun Nairori da Dalolin kasar Amurka wajen yin carbi da suka rataya a wuya kamar sarka.

Ango da Amarya sun rataya carbin takardar Naira da Dala a wurin bikinsu

Ango da Amarya sun rataya carbin takardar Naira da Dala a wurin bikinsu
Source: Twitter

Duku da yin hakan alama ce ta almubazzaranci da alfahari, ta na iya yiwuwa ango da amaryar sun yi hakan ne domin nuna farincikinsu da burge jama'a.

Hotunan sun ja hankalin wasu 'yan Najeriya da suka bayyana rashin jin dadinsu a kan abinda Amarya da suka yi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta kwace rijiyoyin man fetur 6

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewar irin wadannan abubuwa na fariya da almubazzaranci da masu arziki ke yi na daga cikin abinda ke tunzara wasu talakawa su zama 'yan ta'adda.

Najeriya na daga cikin sahun gaba a kasashen duniya dake da yawan talakawa da ko ciyar da kansu basa iya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel