Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Fasto

Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Fasto

- Wata shahararriyar Fasto ta bayyana wasu dalilanta dake nuna cewa duk mutumin da yake cin kifin ruwan teku ba zai shiga aljanna ba

- Ta ce kifayen dake cikin teku suna da alaka da aljannun ruwa

Wata shahararriyar Fasto ta fito ta bayyana cewa duk mutanen da suke cin kifi sadin baza su taba shiga aljanna ba idan suka mutu.

Shahararriya Faston ta bayyana hakan ne a lokacin da da take gabatar da wa'azi ga mabiyanta, Limamiyar ta kuma bayyana mabiyan nata cewa duk mutanen da suke cin abubuwan da suka fito daga ruwan teku, irinsu kifi da sauransu to baza su taba shiga aljanna ba idan suka mutu.

Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Fasto

Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Fasto
Source: Facebook

A yadda wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta ya nuna, Limamiyar ta bayyana cewa kifi sadin ya fito daga cikin ruwan teku ne saboda haka yana da dangantaka da aljannun cikin teku.

A karshe Faston ta bayyana cewa duk masu cin irin wannan kifi suna bukatar taimako sosai kafin su shiga aljanna.

KU KARANTA: Ba dolene sai mata sun sanya Hijabi a Saudiyya ba - Yarima Salman

Malaman addini dai suna cin karen su babbaka a yankin nahiyar Afirka, inda kowanne yake kokarin nunawa mabiyansa cewa shima yana da wata baiwa ta musamman da Allah ya bashi.

Akwai rahotanni da dama da majiyarmu Legit.ng ta kawo akan malaman addini musamman na addinin Kirista wanda ke nuna yadda malaman ke gabatar da mulki son ransu akan mabiyan nasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel