Buhari ya soki masu yiwa talakan Najeriya bukulu

Buhari ya soki masu yiwa talakan Najeriya bukulu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara nanata alkawarin cewar talakan Najeriya zai ci moriyar mulkinsa a zango na biyu tare da yin Alla-wadai da wasu 'yan bukulu da suka hana 'yan Najeriya damar da suke da ita a zaben da ya gabata.

Kazalika ya yaba wa hukumar zabe ta kasa (INEC) bisa kyakykyawan aikin da ta yi duk da kalubalen da ta dan samu da farko tare da yi wa masu zabe godiya a kan juriya da yarda da tsarin dimokradiyya da suka nuna.

A cewar sa; "kafin zaben shekarar 2019, 'yan bukulu basu taba bawa Najeriya damar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba. Amma duk da haka, Najeriya ta samu nasarar shawo kan kalubalen ta a siyasance.

"Jama'ar Najeriya sun nuna kishin kasa ta hanyar barin kasuwancinsu domin fita su sauke hakkinsu na 'yan kasa dake da ikon zaben shugabannin da suke so.

Buhari ya soki masu yiwa talakan Najeriya bukulu
Buhari
Asali: Twitter

"Ina son yin amfani da wannan dama domin sake tabbatar wa da da dukkan 'yan Najeriya cewar sadaukarwa da kuka nuna ta sake zabe na ba zata tashi a banza ba. Zan tabbatar da cewar talakawan Najeriya masu kada kuri'a sun ci moriyar gwamnati na."

DUBA WANNAN: Kotu ta umarci rundunar soji ta mayar da wani Manjo Janar da ta kora daga aiki

Buhari ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su kasance masu yin aiki da nasihohin da darussan dake cikin watan Ramadana.

Kazalika, ya mika sakon ta'aziyya da jaje ga wadanda aiyukan ta'addanci, musamman na masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga, ya shafa tare da cin al washin cewar gwamnatinsa ba zata lamunci kisan jama'a ba da kowanne irin suna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel