Yadda wani Sojan Najeriya ya zamo zakara a jami’ar Ingila

Yadda wani Sojan Najeriya ya zamo zakara a jami’ar Ingila

A tsaka da zanga-zangar da kungiyar kare hakkin dan adam na duniya ke yi akan kokarin sojojin Najeriya wajen yaki da ta’addanci da kuma zargin cewa rundunar soji bata wani kokari wajen kare hakkin yan kasa, wani sojan Najeriya wanda ya kasance lauya, Manjo Ajibade Azeez Atobatele, da ke karatu kasar Ingila, ya daukaka darajar kasar a idanun duniya.

Ya bambanta kansa ta hanyar gamawa da maki mafi daraja a fannin kare hakkin dan adam na kasa da kasa da kuma dokar ta’addanci.

Jami’in sojan na Najeriya ya kuma samu lambar yabo mafi daraja a sashin al’adu da kimiyar zamantakewa, a jami’ar Lancaster, daya daga cikin manyan jami’a 10 a kasar Ingila.

An karrama shi ne a wajen bikin yaye dalibai na jami’ar, wanda aka gudanar a kasar Birtaniya.

Hakazalika, daraktan karatun digiri na uku a sashin shari’a na jami’ar Lancaster, Farfesa Sigrun Skogly, ta tabbatar a wata wasika zuwa ga ofishin jakadancin Najeriya a Landan, cewa kokarin sojan da kuma samun maki mafi daraja da yayi ya zamo abun alfahari domin a cewarta ba kasafai jami’ar ke bayar da irin wannan karramawa ba.

KU KARANTA KUMA: Duk abinda zai faru ya faru: Tsohon ministan Jonathan ya kamo danyar dawowa Najeriya

Makarantar shari’an ta kuma tabbatar da cewa an ba Atobatele gurbin ci gaba da diiri na uku domin ya kara fadada bincike akan lamuran sari’a da ke kewaye da yaki da ta’addanci a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel