An so shugaba Buhari ya cire ni daga minista, saboda ana tunanin ni dan kungiyar asiri ne - Dalung

An so shugaba Buhari ya cire ni daga minista, saboda ana tunanin ni dan kungiyar asiri ne - Dalung

- Na fuskanci kalubale da dama lokacin dana hau kujerar minista

- Sai da aka rubutawa shugaban kasa takarda akan ya cire ni saboda ana tunanin ni dan kungiyar asiri ne

Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya ce mutane sun dameshi kuma sun tsorata shi a lokacin da ya hau kujerar shi ta minista a shekarar 2015.

Yayi bayanin ne jiya Litinin a Abuja a lokacin da aka ma'aikatar matasa da wasanni ta kasa ta hada wani biki saboda shi.

An so shugaba Buhari ya cire ni daga minista, saboda ana tunanin ni dan kungiyar asiri ne - Dalung

An so shugaba Buhari ya cire ni daga minista, saboda ana tunanin ni dan kungiyar asiri ne - Dalung
Source: UGC

"Ba dadewa da bani kujerar minista, kungiyar kare hakkin dan adam ta rubutawa shugaban kasa takarda akan ya cire ni, saboda suna zargin cewa ina daya daga cikin 'yan kungiyar asiri.

"Hakika, a matsayina na lauya, ina iya samun miliyoyin kudi da wannan labari da suka bayar, amma sai nayi hakuri na mance.

"Shekaru uku da rabi dana cinye ina minista na ji dadin su kwarai da gaske. Akwai abubuwa masu rikitarwa a harkar wasanni. Akwai kuma masu ban sha'awa a cikin duk abinda mutum yake so yayi a bangaren wasanni," in ji shi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye

Ya kuma yi magana akan ma'aikatan wasanni da irin kalubalantar shi da suke akan duk wani aiki da yayi.

Ministan Solomon Dalong yana daya daga cikin ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi mulki da su a wa'adinsa na farko, sai dai har yanzu ba a san matsayin da yawa daga cikin ministocin ba, inda shugaban kasar ya bayyana cewa zai wuce da yawa daga cikin su amma har yanzu bai bayyana ko su wanene zai wuce da su din ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel