Wata kwamiti a jihar Bauchi ta kaiwa gwamnan jihar wani tsari data binciko da zai taimaka wurin samar da ayyukan a jihar

Wata kwamiti a jihar Bauchi ta kaiwa gwamnan jihar wani tsari data binciko da zai taimaka wurin samar da ayyukan a jihar

-Wata kwamiti ta nemo hanyar da za ta taimaka wurin samawa jihar Bauchi kudaden shiga

- Sannan kwamitin tace ta kuma samo hanyar da za ta samawa al'ummar jihar ayyukan yi

Wata kwamiti mai bada shawara akan tattalin arziki wacce sabon gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed Kaura ya kafa, ta kaiwa gwamnan jihar wata hanya da ta binciko wacce zata taimaka wurin samarwa da gwamnatin jihar kudaden shiga masu tarin yawa.

Shugaban kwamitin, Farfesa Usman Bugaje, a lokacin da yake sanar da binciken nasu a Bauchi, ya ce binciken nasu kuma ya samu wata hanya da za abi domin samarwa da aal'ummar jihar ayyukan yi.

"Abinda muke dashi a nan shine, hanyoyin da zasu taimaka maka wurin gabatar da mulkin ka na shekara hudu a wannan jihar.

Wata kwamiti a jihar Bauchi ta kaiwa gwamnan jihar wani tsari data binciko da zai taimaka wurin samar da ayyukan a jihar
Wata kwamiti a jihar Bauchi ta kaiwa gwamnan jihar wani tsari data binciko da zai taimaka wurin samar da ayyukan a jihar
Asali: Facebook

"Muna shawartar ka daka yi iya bakin kokarin ka wurin gabatar da wannan tsari, ta hanyar amfani da amintattun mutanen ka."

Harkar noma hanya ce da jihar Bauchi take da kasa mai kyau fiye da wasu jihohi a kasar nan, saboda haka muna shawartar ka a matsayinka na gwamna da ka bai wa bangaren noma muhimmanci.

"Nan da shekara biyu muna so jihar Bauchi ta zama dayaa daga cikin jihohin da zasu dinga fitar da kayan gona zuwa kasashen duniya," in ji Bugaje.

KU KARANTA: Yadda wayar salula ta yi sanadiyyar mutuwar wani saurayi

A lokacin da yake karbar rahoton, gwamnan jihar yayi alkawarin tabbatar da dukkan ayyukan da kwamitin ta bukaci yayi.

Gwamnan kuma yayi alkawarin sanya mutane masu kula a bangaren noma domin kawo cigaba a fannin noma a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel