Wata mata ta bayyana yadda ta yi mutuwar karya yayin da 'yan bindiga suka kashe duka danginta a jihar Filato
- Wata mata ta bayyana yadda ta sha da kyar lokacin da 'yan bindiga suka shigo har cikin gidansu suka kashe duka danginta akan idonta
- Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun kashe kowa aa gidan banda wata jaririya da suka tausaya mata, sai kuma mataar da tayi mutuwar karya
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane shida 'yan gida daya a kauyen Dangwal dake kan hanyar Jos zuwa Kaduna, cikin karamar hukumar Riyom dake jihar Filato, a daren ranar Litinin 27 ga watan Mayu.
A rahoton da muka samu, 'yan bindigar sun shiga kauyen Dangwal ranar Litinin da misalin karfe 8 na dare, inda suka wuce kai tsaye zuwa gidan Lo-Gwong Du, suka kashe mutane shida.
Lokacin da take magana da manema labarai, daya daga cikin 'yan uwan wadanda aka kashe din, Lyop Gideon, mai shekaru 25 ta bayyana cewa ita ma ta tsira da ranta ne bayan tayi mutuwar karya lokacin da 'yan bindigar suke harbin su.
Hakazalika jaririyar matar ita ma ta tsira da ranta, bayan 'yan bindigar sun tausaya mata basu kasheta ba, wacce a lokacin take hannun kakarta. Sai dai kuma sun kashe kakar yarinyar, mijin Lyop, iyayen shi, da 'yan uwanshi guda uku.
"Na kwanta a kasa ne lokacin da suke harbin mu, yayin da suka kashe kowa a gidan. 'Yata tayi ta ihu a lokacin da take hannun kakarta, amma cikin ikon Allah babu abinda ya sameta," in ji matar.
KU KARANTA: Rikicin siyasar jihar Kano: An yi mana fashin mulki - Sanata Kwankwaso
A cewar ta dukkansu suna cikin cin abinci da dare ne lokacin da 'yan bindigar suka afka musu.
"Mijina yana cikin dakin mu a lokacin da 'yan bindigar suka zo, shi suka fara harbi, sai suka shigo dakin da muke zaune mu bakwai, daya daga cikin su yayi kokarin yayi magana cikin yaren Berom amma bai iya ba sosai. Amma kuma yayi magana cikin harshen Fullanci, inda ya ce 'Hurut mu hilleh' bayan sun fara harbin mu, amma ban tunanin ya iya Fullancin sosai ma."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng