Gwamnonin PDP na kudu maso gabas da Obiano sun taya Buhari murna

Gwamnonin PDP na kudu maso gabas da Obiano sun taya Buhari murna

- Kungiyar gwamnonin jam' iyyar Peoples Democratic Party PDP na yankin kudu maso gabas sun aika sakon taya murna ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan rantsar dashi da aka yi a jiya Laraba, 29 ga watan Mayu

- Gwamna Willie Obiano na jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) ma ya taya shugaban kasar murna

- Sun nuna karfin gwiwa akan yunkurin Buhari na wanzar da farin ciki a zukatan yan Najeriya a wannan mulki nasa na biyu

Ga dukkan alamu abubuwa sun tabarbare a sansanin tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, biyo bayan sakon taya murna da kungiyar gwamnonin PDP a yankin kudu maso gabas suka aika wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan rantsar dashi da aka yi a jiya Laraba, 29 ga watan Mayu.

Kungiyar wanda gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi ke shugabanta, na dauke da Willie Obiano (Anambra), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Okezie Ikpeazu (Abia) da Emeka Ihedioha, sabon gwamnan jihar Imo da aka rantsar.

Gwamnonin PDP na kudu maso gabas da Obiano sun taya Buhari murna

Gwamnonin PDP na kudu maso gabas da Obiano sun taya Buhari murna
Source: UGC

Banda Obiano ne kadai mamban a jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) duk sauran gwamnonin sun ci zabe ne a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya yabawa Saraki a kan wani abu daya da yayi a kan mulki

Kungiyar ta mika sakon taya murnarta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a jaridar National Daily tare da kyautata zatton su a yunkurinsa na tabbatar da cewa yan Najeriya sunyi farin ciki a mulkinsa na biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel