Tsohuwa yar shekara 100 ta rasu tare da yayanta 3 bayan sun ci guba a abinci

Tsohuwa yar shekara 100 ta rasu tare da yayanta 3 bayan sun ci guba a abinci

Rundunar Yansandan jahar Ebonyi ta sanar da mutuwar wasu mata guda hudu sakamakon cin abinci mai dauke da nau’in guba a kauyen Amaechara cikin karamar hukumar Afikpo na jahar Ebonyi, daga cikinsu har da tsohuwa yar shekara 100.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai matukar tayar da hankali ya faru ne a ranar Lahadin data gabata, bayan tsohuwar tare da yayanta mata guda biyu da yar aikinsu sun kammala cin abincin dare.

KU KARANTA: Farawa da iyawa: Wani sabon gwamna yace ba zai iya biyan albashin N30,000 ba

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, Loett Odah ta bayyana cewa “Mutuwar tasu ta faru ne sakamakon cin gubar abinci, samun rahoton keda wuya muka aika da jami’anmu zuwa gidan, inda suka tarar da gawarwakin mutanen.

“Daga cikinsu akwai tsohuwa mai shekaru 100 da aka gano gawarta akan gado, sai diyarta wanda tsohuwar malamar makarantace da aka gano gawarta a falo, haka zalika kanwarta, da kuma yar aikinsu da aka gano gawarta a dakin girke girke.” Inji kaakaki Lovett.

Kaakakin ta kara da cewa sun mika gawar mamatan zuwa dakin ajiyan gawarwaki na asibitin Matter dake kauyen Amaechara cikin karamar hukumar Afikpo ta Arewa.

Daga karshe jami’ar Yansanda Odah Lovett tace tuni rundunar Yansandan jahar Ebonyi ta kaddamar da binciken kwakwaf akan lamarin don gano musabbabin wannan ibtila’i.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel