Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

A ranar Laraba shugaba Muhammadu Buhari ya fito a sabuwar motarsa kirar Mercedes-Maybach s650 da harsashi baya huda ta wadda masana suka kiyasta kudin ta a kalla Naira MIliyan 280.

A kasafin kudin 2018, an ware Naira Miliyan 907 domin sayan sabbin motocci da kayan motocci na tawagar shugaban kasa yayin da a kasafin kudin 2019 an ware Naira MIliyan 843 domin saye da kulawa da motoccin da ke yiwa shugaban kasar rakiya.

A ranar Laraba, wata kafar yada labarai na yanar gizo tayi kuskuren kiyasta kudin motar Mercedes-Maybach s650 na shugaba Buhari kan zunzurutun kudi $170,000 wato Naira Miliyan 61.

Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari
Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

Sai dai wani dalilin manyan motoccin alfarma da ya yi kwangilar sayarwa fadar shugabansa motocci a baya ya shaidawa Daily Nigerian cewa sabuwar motar da shugaba Muhammadu Buhari ya shiga Mercedes-Maybach s650 na shekarar 2019 ne.

A cewarsa, idan a kamfani aka sakawa motar garkuwar hana harsashi huda ta, kudin ta na iya kaiwa Naira Miliyan 360. "Ko da daga bisani aka saka mata gilashi wadda harsashi baya hudawa, kudin motar yana iya kaiwa kimanin Naira Miliyan 288.

"Kudin saka gilasai masu hana harsashi huda mota na Mercedes-Maybach s650 ya kan kai Naira Miliyan 80. Irin wadannan motoccin suna da matukar tsada ko garegaren tayar motar su kan kai kimanin Naira Miliyan 10.8 kowannen su." inji Masanin.

Ya kuma kara da cewa a lokacin da aka rantsar da Buhari kan mulki karo na farko, ya saka takunkumi kan sayan sabbin motocci na tawagar shugaban kasa.

"An dage takunkumin saboda motoccin da ya gada daga magabacinsa sun fara samun matsalar inji ko na tsaro," a cewar majiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel