Tafiyar Singham: Kalli sabon kwamishinan Yansanda da aka tura Kano

Tafiyar Singham: Kalli sabon kwamishinan Yansanda da aka tura Kano

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya tura babban jami’in Dansanda Ahmed Iliyasu zuwa Kano a matsayin sabon kwamishinan Yansandan jahar da zai maye gurbin Kwamishina Wakili Mohammed Singham daya yayi murabus.

Kwamishina Singham, ko ace Maza kwaya Mata kwaya yayi murabus daga aikin Dansanda ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu bayan kwashe shekaru 35 yana aikin Dansanda tare da sadaukar da rayuwarsa wajen bauta ma kasa Najeriya.

KU KARANTA: Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato

Tafiyar Singham: Kalli sabon kwamishinan Yansanda da aka tura Kano

Iliyasu
Source: Facebook

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, DCP Frank Mba ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, inda yace kafin nadinsa, iliyasu shine jami’I mai ladabtar da Yansanda a shelkwatan Yansandan Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa Iliyasu yana da digiri na biyu na fannin tafiyar da kasuwanci wanda ya samu daga jami’ar Ambrose Ali dake garin Ekpoma jahar Edo, haka zalika ya taba rike mukamin kwamishinan Yansandan jahar Ogun daga 2016 zuwa 2019.

Daga karshe kaakakin yace babban sufetan Yansanda na taya SInghma murnar ajiye aiki lami lafiya tare da yi masa fatan alheri yayin da yayi murabus, sa’annan yayi kira ga Iliyasu ya dage wajen daurawa a inda Singham ya tsaya a jahar Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel