Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau

Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau

A yau Juma’a, 24 ga watan Mayu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da sallar Juma’a a babban masallacin kasa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasar zai gabatar da sallar Juma’a a masallacin ne daga cikin tsare-tsare da aka shirya na rantsar da shi a karo na biyu.

Za a rantsar da shugaba Buhari a karo na biyu a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu a dakin taro na Eagle Square da ke birnin tarayya, Abuja.

Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau
Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau
Asali: Facebook

Idan za a tuna yan shekarun baya, Shugaban kasar ya daina yin sallar Juma’a a babban masallaccin kasar. Shugaban kasar yayi bayanin cewa hukunci ya kasance ne domin guje ma takurar da zirga-zirgan Shugaban kasa zai haddasa wa mutane.

Shugaban kasar kan gudanar da sallar Juma’a ne a masallacin fadar Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya soke bikin ranar 29 ga watan Mayu

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, ta kaddamar da ranar Laraba, 29 ga watan Mayu da kuma 12 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin bikin rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ranar Damokradiyya.

Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai gabannin rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel