Ana biya na naira 180 ana saduwa dani - Fatmata

Ana biya na naira 180 ana saduwa dani - Fatmata

- Bincike ya nuna cewa an samu yawaitar karuwai a kasar Saliyo tun lokacin da cutar Ebola ta bulla a kasar

- Sama da mata 300,000 ne suke karuwanci a fadin kasar ta Saliyo

- 'Yan mata da yawa a kasar suna shiga harkar karuwanci domin su rayu

A wata hira da manema labarai suka yi da wasu 'yan mata guda biyu a kasar masu suna Mariam da Fatmata sun bayyanawa manema labaran yadda ake saduwa da su a kowanne kwana daya inda ake ba su Leone 5,000 wato kimanin naira 180 a kudin Najeriya.

Ana biya na naira 180 ana saduwa dani - Fatmata
Ana biya na naira 180 ana saduwa dani - Fatmata
Asali: Facebook

Ga yadda hirar ta su ta kaya da Fatmatu Kanu, 'yar shekara 18 a duniya:

"Babu yadda zan yi na ci abinci idan ban fita na nemi maza a titi ba, maza suna cewa suna bukata ta, sukan kaini gidajensu inda suke kwanciya dani gaba daya ranar sai su bani Leone 5,000, wato kimanin naira 180.

"Inda mahaifiyata ba ta mutu sanadiyyar Ebola ba, da ban shiga wannan harkar ba. Daga karshe ba ta samu ta yi komai ba, ko magana ba ta iya yi."

Fatmata ta ce tana saduwa da maza bakwai zuwa takwas a dare daya.

"Wasu lokutan muna yin jima'in minti biyu domin samun Leone 5,000 wato naira 180, sannan farashin yana kai wa Leones 50,000 wato naira 1800.

"Ina da kanne guda biyu, kuma ni ke kula da su, idan na fita na samu kudi, ni nake biya musu kudin makaranta.

"Ina so na yi karatun likita na bangaren masu karbar haihuwa, wannan shi ne fatana tun ina yarinya karama."

Hasashe ya nuna cewa kimanin mata 300,000 ne ke karuwanci a kasar Saliyo.

KU KARANTA: Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3

Wata da manema labaran suka yi hira da ita mai suna Mariama Fofanah, 'yar shekara 20 a duniya, ta bayyana yadda ta fara harkar karuwanci:

"Ina 'yar shekara 14 na fara karuwanci, mahaifiyarmu ce ta sanya mu a cikin wannan hali saboda ba ta iya kula damu. Tana yawan cewa mu shegu ne.

"Akwai wani lokaci a baya da na samu wani mutumi mun yi ciniki da shi sosai. Bayan ya gama saduwa dani, sai ya ki ba ni kudina, sai ya gudu da kudina da kuma wayata. Nayi kokarin rigima dashi, sai ya doke ni a fuska, inda ya ji mini ciwo sosai ya gudu kuma."

Kungiyoyin ba da agajin gaggawa sun ce ana kara samun karuwai a kasar tun barkewar cutar Ebola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng