Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95

Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95

- Ma'aikatan jihar Kano sun shiga halin dar-dar bayan gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95 daga bankin musulunci

- Gwamnan ya ce ya ciyo bashin ne saboda ya habaka fannin noman rani da kiwo a fadin jihar

Ma'aikatan gwamnatin jihar Kano sun tsorata, bayan gwamnatin jihar ta bayyana cewar taa ciyo bashin dala miliyan 95 daga gurin bankin musulunci na duniya dake kasar Saudiyya, domin kara habaka fannin noman rani a fadin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Nasiru Umar Gawuna shine ya bayyana haka a lokacin daya karbi bakuncin wasu mutane a gidan gwamnatin jihar jiya Laraba.

Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95
Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95
Asali: Facebook

A cewarsa, jihar wacce take da kyakkyawar kasar noman rani a fadin Najeriya, na bukatar a habaka fannin, domin samun cigaba a fadin jihar.

"Dawowa ta kenan daga kasar Saudiyya inda muka samu nasarar karbo bashin dala miliyan 95, kuma zamu yi amfani da kudin wurin kawo cigaba a fannin noman rani.

"Dama an riga an san mune muke da cigaba a fannin kasuwanci a yankin Afirka ta Yamma.

"Duk wanda ya ke fitar da citta, ko zobo dama kowanne irin sai ya zo Kano ya saya an gyara mishi kafin ya samu ya fitar dashi saboda komai ana yin shi a Kano.

KU KARANTA: An cafke wani limami da yake kokarin sace wani yaro dan shekara 11

"Sannan zamu yi amfani da wani bangare na kudin wurin habaka fannin kiwo."

Tsoro ya shiga zukatan ma'aikatan jihar, bayan sun samu labarin ciyo bashin da gwamnatin tayi. Saboda sun san cewa yanzu haka ana sauraron karar zaben gwamnan jihar a kotu, mutane musamman wadanda suka dogara da gwamnatin jihar wurin samun albashi sun fara tsorata da tsarin gwamnan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel