Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba a kan IGP Mohammed Adamu

Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba a kan IGP Mohammed Adamu

A ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da Mohammed Abubakar Adamu a matsayin shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP) mai cikakken iko.

Ga wasu muhimman abubuwa 5 a kan sabon IGP Adamu da ba lallai kun san da su ba:

1. Yana da takardar shaidar digiri a kan 'Geography' daga jami'ar garin Porsmouth dake kasar Ingila

2. An bashi kyautar kwamishinan 'yan sanda mafi kwazo a Najeriya a shekarar 2015

3. Ya samu digirin girmamawa na uku (PhD) a fannin 'International Relations' daga jami'ar Godsfrey Okoye dake jihar Enugu.

4. 'Ya'yan sa biyu, Salmanu Mohammed Adamu da Nafisatu Mohammed, sun yi aure a rana guda a garin Lafiya a jihar Nasarawa.

5. Ya kware a yaren Turanci da Faransanci

A ranar 15 ga watan Janairu ne shugaba Buhari ya nada Mohammed Adamu a matsayin shugaban rundunar 'yan sanda na rikon kwarya bayan lokacin ritayar tsohon IGP Ibrahim Idris ya cika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel