Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3

Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3

- Bayan ya shafe shekaru har guda takwas yana mulkin, jihar Nasarawa, gwamnan jihar Tanko Al-Makura ya je yana rokar zababben gwamnan jihar akan ya kara masa wa'adin watanni uku

- Ya ce da zai samu ya kara masa watannin da ya kammala ayyukan alkairin da ya fara ga al'ummar jihar

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo da ya faru jiya Laraba a gidan gwamnatin jihar Nasarawa dake Lafiya, a lokacin da gwamnan jihar mai barin gado Alhaji Umar Tanko Al-Makura yake rokar sabon zababben gwamnan jihar, Abdullahi Sule, akan ya kara masa wa'adin wata uku domin ya kammala ayyukan da yayi alkawari ga al'ummar jihar.

Hakan ya faru a lokacin da ake nada sarakuna goma sha shida da wasu manya a fadin jihar.

Gwamnan mai barin gado ya ce: "Saboda manufata ta son ganin jihar nan ta cigaba, shekaru takwas da nayi basu isheni ba; ina ma ace zababben gwamna zai kara mini wa'adin wata uku.

Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3

Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3
Source: UGC

"Da ba dan dokar kasa ta hana ba, dana roki zababben gwamna ya ara mini wa'adin watanni uku domin na kammala ayyukan alkhairi dana sanyo gaba."

Ya shawarci al'ummar jihar da su hade kansu, su cire bambancin addini da al'ada, suyi aiki tare domin kawo cigaba ga jihar ta Nasarawa.

KU KARANTA: PDP ta bukaci Lai Mohammed ya roke ta gafara

Gwamnan mai barin gado ya ce nadin sarakunan gargajiyar guda goma sha shida dama ya dade yana son gabatar da shi.

Ya ce an samu jinkirin nadin ne saboda matsalar rikicin makiyaya da manoma da ake ta fama dashi a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel