Nade-naden mukamai: Bincike ya nuna Buhari ya fifita kudu sama da arewa

Nade-naden mukamai: Bincike ya nuna Buhari ya fifita kudu sama da arewa

- Wasu bayanai da suka billo sun kalubalanci ikirari da zargin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa yan arewa mukamai fiye da yan kudu

- Binciken da takardu sun bayyana cewa akwai daidaito wajen rabon manyan mukamai da fadar Shugaban kasa tayi ga yankunan biyu

- Takardun sun nuna cewa jihar Ogun ce a sama tare da mukamai 31, fiye da nade-naden da jihohin arewa maso yamma uku suka samu a hade

Sabanin shahararren hasashen nan da ke yawo, bincike da hujjoji da suka billo sun nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yankin kudu manyan mukamai masu maiko a kasar fiye da yanda yayi a arewa.

Takardu da ke kunshe da nade-naden da Shugaban kasa Buhari yayi a gwamnatinsa na farko a 2015 ya nuna cewa akwai daidaito tsakanin yankunan biyu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Misali, jihar Ogun ce a saman jarin mukaman inda take da nade-nade 31, fiye da nade-naden da jihohin arewa maso yamma uku ke dashi wanda suka hada da Kebbi 13, Zamfara bakwai da kuma Sokoto mai shida.

Nade-naden mukamai: Bincike ya nuna Buhari ya fifita kudu sama da arewa
Nade-naden mukamai: Bincike ya nuna Buhari ya fifita kudu sama da arewa
Source: Depositphotos

A arewa maso yamma, jihar Katsina ce da mukamai mafi yawa guda 24, yayinda Kaduna da Kano suka samu 16; inda Jigawa ke da 12.

KU KARANTA KUMA: Muna da tabbacin nasarar Atiku a kotun zaben Shugaban kasa - PDP

Inda a nade-naden siyasa kudu maso gabas ce keda mafi karanci, Imo ce ta uku a nadin MDA (nade-nade 29), sannan aka bai wa Anambra 20 inda Abia ta samu 14.

Jihohi kamar su Enugu da Ebonyi na da takwas da bakwai. Sai dai kuma, takardu dun nuna cewa yawan nade-naden shugabanni a ma’aikatu, kaso 51 cikin dari ya tafi ne ga jihohin arewa 19, sannan kaso 49 cikin dari ya tafi ga jihohin kudu 17.

A daya bangaren, manyan nade-naden siyasa 124 kamar irin su masu bayar da shawara na musamman, manyan masu bayar da shawara, da kuma hadimai na musamman ga Shugaban kasa sun kasance 59 daga arewa sannan 65 daga kudu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel