Bisa kuskure na shake budurwa ta har ta mutu - Saurayi

Bisa kuskure na shake budurwa ta har ta mutu - Saurayi

A ranar Talatar da ta gabata ne wani mutum mai suna Kelechukwu Chukwuanugo ya shaida wa wata babbar kotun jihar Legas dake unguwar Igbosere cewar bisa kuskure ne ya shake wuyan budurwar sa, Lizzy Nzewi, yayin koka wa a kan wayar hannu, amma sai ta mutu.

Cikin hawaye, Chukwuanugo, mai shekaru 37, ya fada wa alkalin kotun, Jastis Adedayo Akintoye, cewar yana matukar son Nzewi kuma bashi da niyyar kashe ta.

Gwamnatin jihar Legas ce ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhumar sa da aikata laifin kisan kai.

Lauya mai gabatar da kara, Yusuf Sule, ya ce Chukwuanugo ya shake wuyan Nzewi da zanin atamfa da misalin karfe 2:00 na safiyar ranar 19 ga watan Yuli na shekarar 2014, a gidan su mai lamba 34 dake rukunin gidajen 'Green Estate' a unguwar Amuwo-Odofin a garin Legas.

Ya sanar da kotun cewar jami'an 'yan sandan Najeriya dake aiki a kasashen ketare (INTERPOL) ne suka cafke Chukwuanugo a kan iyakar kasashen Ghana da Kwadebuwa bayan ya gudu da motar marigayiyar kirar 'Range Rover Sports Utility Vehicle, SUV'.

Bisa kuskure na shake budurwa ta har ta mutu - Saurayi

Bisa kuskure na shake budurwa ta har ta mutu - Saurayi
Source: Twitter

Da yake kare kan sa a gaban kotun, Chukwuanugo ya bayyana cewar ya fara haduwa da Nzewi ne a kasar Ghana a shekarar 2012 lokacin da take yawan yin siyayya a wani kamfani da yake aiki.

Ya ce tun daga lokacin suka yi sabon da ya kai su da kulla abota sakamakon shakuwar da suka yi da juna cikin dan kankanin lokaci, shi da Nzewi, wacce dama bazawara ce har da 'ya'ya hudu.

Ya cigaba da cewa hatta lokacin da zasu dawo Najeriya, sun yi takaradar fasfo da suna iri daya, tamkar mata da miji, tunda dama suna da niyyar yin aure.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisa: Buba ya janye wa Gbajabiamila

Chukwuanugo ya shaida wa kotun cewar wata rana ne Nzewi ta fita tayi dare sosai ba ta dawo gida ba kuma duk kiran da ya yi mata bata amsa ba. Ya ce, bayan ta dawo, ta shiga wanka sai aka kira ta a waya, shi kuma ganin hoton namiji ne ki kira sai ya dauko don sanin ko waye, amma kafin su yi magana sai Nzewi tayi zumbur ta fito daga bandaki tare da kokarin kwace wayar ta daga hannun sa.

Ya ce sakamakon kokawar da suke yi ne ta jawo ya shake mata wuya bayan ta kama masa mazakuta. Ya kara da cewa bayan sun fadi suna kokawar ne sai ya fahimci ya ji ciwo, sai ya hakura ya tafi bandaki domin ya wanke wurin, amma bayan ya fito sai ya ga Nzewi bata motsa ba daga inda ya bar ta, kuma bayan ya zo ya duba ta sai yaga bakinta yana fitar da wata kumfa.

A cewar sa, sakamakon rudewar da ya yi ne sai kawai ya dauki katin ATM da makulllin motar ta ya gudu daga gidan cikin tashin hankali da dimuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel