'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 14 a jihar Nasarawa

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 14 a jihar Nasarawa

Jaridar Vanguard ta tabbatar da cewa, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Nasarawa, ta samu nasarar cafke miyagun mutane 14 da suka addabi al'ummar jihar da mummunan ta'addancin garkuwa da mutane.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bola Longe, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin gabatar wa da manema labarai jerin miyagun 'yan ta'adda 14 cikin birnin Lafiya a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu.

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 14 a jihar Nasarawa

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 14 a jihar Nasarawa
Source: UGC

Longe ya yi bayanin cewa rundunar 'yan sanda ta samu nasarar cika hannun ta dumu-dumu da 'yan ta'adda yayin wani simame na kwanton bauna da ta kai moboyar su a Mararraban Udege da ke karkashin karamar hukumar Toto ta jihar.

A yayin bayar da tabbacin tsayuwar dakan sa ga al'ummar jihar Nasarawa wajen tsarkake ta daga dukkanin wani nau'i na ta'ada, Longe ya ce a halin yanzu bincike zai ci gaba da gudana akan masu ta'adar da suka shiga hannu domin gurfanar da su gaban Kuliya.

KARANTA KUMA: Mai daki na ta hana ni kusantuwa da ita saboda ƙanƙantar Mazakuta - Fasto ya shaidawa Kotu

sCikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar 'yan sanda ta yiwa manema labarai bajakolin wasu miyagun 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna bayan ta samu nasarar sheke gogarman dan ta'adda, Sule Shaho.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel