Sojojin Najeriya sun cafke masu garkuwa da Bayin Allah 49 a Jihar Taraba

Sojojin Najeriya sun cafke masu garkuwa da Bayin Allah 49 a Jihar Taraba

Labari ya kai gare mu cewa Sojin Najeriya sun cafke wasu mutane 49 da ake zargi da laifin garkuwa da mutane. An kama wadanan mutane ne a cikin babban Dajin nan na Kashimbila a jihar Taraba.

Wani Bawan Allah Mazaunin wannan yanki da ke cikin karamar hukumar Takum a Taraba, ya bayyana cewa Dakarun Sojojin na Najeriya sun iso jejin ne a cikin wani jirgin yaki mai saukar ungulu.

Mista Bulus Gampi ya sanar da manema labarai cewa wadannan Rundunar Sojoji sun zo ne daga birnin Abuja domin kawo dauki a wannan Yankin da yayi fice da satar jama’a, ana garkuwa da su.

A cewar Bulus Gampi, Gawurtaccen ‘dan bindigan nan da ake kira Gana yana zaune ne cikin wannan Daji na Kashimbila tare da Yaransa. Wannan jeji yana kan iyaka tsakanin Benuwai da Taraba.

KU KARANTA: An budewa wasu masu kallon kwallo wuta a Garin Jos

Gampi yake cewa babu tabbacin cewa Gana yana cikin wadanan mutane kusan 50 da aka kama kwanan nan, amma yace jejin ne mafakar wadannan gagararen ‘dan bindiga da ya fito daga Benuwai.

Tuni dai an wuce da wadannan mutane da aka cafke zuwa birnin tarayya Abuja. Rundunar Sojojin da ke Abuja ne su ka taimakawa Dakarun Sojin da ke Barikin Tukum wajen kai wannan hari a Dajin.

Ko da aka tambayi ‘yan sanda a game da wannan nasara da jami’an tsaro su ka samu, sun bayyana cewa ba su da masaniya. Kakakin ‘yan sandan Taraba, DSP David Misal yace wannan aikin soji ne zalla.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel