Anci moriyar ganga: Mun zabeka amma ka manta damu – Kutaren Najeriya ga Buhari

Anci moriyar ganga: Mun zabeka amma ka manta damu – Kutaren Najeriya ga Buhari

Kungiyar kutaren Najeriya mazauna kauyen Alheri dake Yangoji cikin karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayya Abuja ta bayyana damuwarta da rikon sakainar kashin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke musu duk kuwa da cewa sun bashi gagarumar gudunmuwa a zaben 2015 da 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dakacin kauyen, Ali Isa ne ya bayyana haka a ranar Asabar 18 ga watan Mayu yayin da yake karbar kyautan kayan abinci a madadin jama’ansa da gidauniyar tallafi ta kasar Qatar ta kai musu.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun bude masu kallon kwallo wuta a garin Jos

Shugaba Isa yace sama da shekaru shida kenan basu da wutar lantarki sakamakon sace na’urar Turansufomarsu da aka yi, don haka suke fama da macizai da miyagun halittu da daddare saboda duhun dake mamaye garin idan dare yayi.

Bugu da kari, Isa yace asibiti kwal daya tilo da aka gina musu bashi da wata amfani a wajensu sakamakon babu magunguna a cikinsa, haka zalika ya kara da cewa jama’an kauyen basu samun tallafin taki a lokacin damuna don inganta nomansu.

A wani labarin kuma, akalla mutum guda ne ya rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama suka samu munana raunuka sakamakon wani mummunan hari da wasu yan bindiga suka kai a wani gidan kallon kwallo dake garin Jos na jahar Filato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel