Dalibar 'Yan Matan Chibok ta kammala karatun digiri a kasar Amurka

Dalibar 'Yan Matan Chibok ta kammala karatun digiri a kasar Amurka

Da ya ke dai Hausawa na cewa zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi, mun samu cewa wata daliba, Palmatah Mutah, daya daga cikin 'yan Matan makarantar Sakandire ta garin Chibok ta kammala karatun digiri.

Bikin yaye dalibai a makarantar Northern Community College Virginia, a kasar Amurka inda Palmatah ta kammala digiri

Bikin yaye dalibai a makarantar Northern Community College Virginia, a kasar Amurka inda Palmatah ta kammala digiri
Source: Instagram

A halin yanzu Palmatah mai shekaru 23 a duniya, wadda ta ksance daya daga cikn 'yan Matan makarantar sakandire da kungiyar Boko Haram ta yashe a shekarar 2014 a garin Chibok na jihar Borno, ta samu nasarar kammala karatun digiri a wata kwaleji dake kasar Amurka.

Rabon ganin badi ya sanya Palmatah ta dira daga kan babbar motar da ta yi dakon su yayin da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta yashe su daga makarantar su ta garin Chibok dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

KARANTA KUMA: Aikin Umarah: Bidiyon shugaba Buhari yana sassarfa a tsakanin Duwatsun Safa da Marwa

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, samun nasarar kammala karatun digiri da Palmatah ta yi a kwalejin Northern Virginia da ke kasar Amurka na zuwa ne bayan cika shekaru biyar da wata daya da kuma kwanaki uku da aukuwar ta'addancin mayakan Boko Haram a garin Chibok.

Palmatah da ta kasance mace ta farko daga cikin 'yan Matan Chibok da suka tsere daga hannun 'yan ta'adda, ta samu nasarar kammala karatun ta a fannin nazarin kimiyya yayin da wani fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Emmanuel Ogebe ya dauki nauyin ta tare da wasu 'yan Matan garin Chibok guda tara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel