Gwamna Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri guda 100 a Kano (Hotuna)

Gwamna Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri guda 100 a Kano (Hotuna)

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar gani da ido tare da kaddamar da wasu manyan motoci sufuri guda dari da yake shirin zubasu akan hanyoyin jahar Kano don fara jigilar jama’a da kayansu nan bada jimawa ba.

A ranar Laraba, 15 ga watan Mayu ne Ganduje ya kai ziyarar gani da ido ga manya motocin safa safan, wadanda yace gwamnatin jahar Kano zata zubasu ne akan hanyoyin Gwarzo zuwa Bata da kuma Dawanau zuwa Bata.

Gwamna Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri guda 100 a Kano (Hotuna)

Gwamna Ganduje
Source: Facebook

KU KARANTA: Zargin juyin mulki: Makaryacin banza – Atiku ga Minista Lai Muhammad

Legit.ng ta ruwaito a yayin jawabinsa, gwamnan yace wannan aikin na gwaji ne, saboda gwamnatinsa nada nufin karo wasu motoci domin zubasu akan manyan hanyoyin jahar Kano da dama don rage ma al’ummar Kano wahalhalun samun ababen hawa.

Gwamna Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri guda 100 a Kano (Hotuna)

Gwamna Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri guda 100 a Kano
Source: UGC

Amma gwamnan yace an samar da tsarin sufurin manyan motocin ne a hadaka tsakanin gwamnatin jahar Kano da kamfanin sufuri na Metropolitan Bus Company, yayin da gwmnatin Kano ta bayar da kashi 35, kimanin naira biliyan daya kenan (N1000,000,000), kamfanin kuma ta bayar da kashi 65.

Gwamnan ya kara da cewa nan bada jimawa bane motocin zasu fara aiki akan hanyoyin da aka zayyana, hanyar Gwarzo zuwa Bata da hanyar Dawanau zuwa Bata, sa’annan za’a kammala aikin ware musu hanyoyinsu tare da samar musu da tashoshi da wuraren tsayawa akan titunan cikin watanni uku masu zuwa.

Daga karshe gwamnan ya bada tabbacin motocin zasu fara aiki gadan gadan ne a cikin watan Agustan shekarar 2019. Muma anan muna yi ma Kanawa fatan alheri, da kuma Allah Ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel