Makashinka yana tare da kai: Atiku na cin dunduniyar gwamnatin Buhari – Lai Muhammad

Makashinka yana tare da kai: Atiku na cin dunduniyar gwamnatin Buhari – Lai Muhammad

Gwamnatin Najeriya ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP tare da dan takarar shugaban kasanta a zaben shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar da cin dunduniyar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yi musu bita da kulli.

Legit.ng ta ruwaito ministan watsa labaru na Najeriya, Lai Muhammed ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da yayi da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, inda yace Atiku da PDP sun hade ma Buhari kai suna furta kalaman batanci a gareshi tare da neman tunzura jama’a.

KU KARANTA: Gudaji Kazaure ya bayyana rashin jin dadinsa da sake nada shugaban babban banki

Don haka Minista Lai yayi kira ga Atikun daya daina irin furucin da yake yi wand aka iya tayar da zauni tsaye a Najeriya, tare da dumama farfajiyar siyasar Najeriya, idan ba haka kuma zai sha mamaki muddin ya wuce gona da iri.

Minista Lai ya cigaba da fadin “Gwamnati ta damu kwarai game da cin fuskar bangaren shari’a da jam’iyyar PDP take yi, da kuma bayyanar wata kungiya dake kira ga dakarun Sojin Najeriya dasu yi ma shugaban kasa Buharu juyin mulki.

“Bamu taba ji a tarihin Najeriya inda jam’iyyar adawa da dan takararta na zaben shugaban kasa suka nuna irin kwadayin mulkin da PDP da Atiku Abubakar suke yi ba, musamman tun bayan lallasasu da Buhari yayi a zaben 23 ga watan Feburairu na shekarar 2019.” Inji shi.

Lai ya tuna ma yan Najeriya batun da Atiku yayi kafin zaben inda yace idan har yan Najeriya basu yi awon gaba da APC da Buhari daga mulki ba, tabbas hare haren makiyaya ba zai kare ba, don haka yace Atiku baya rasa masaniya ko hannu cikin kashe kashen da ake yi a yanzu.

Daga karshe Minista Lai yayi kira ga PDP data daina yi ma Najeriya fatan tashin hankali, kamata yayi PDP ta mayar da hankali wajen neman hakkinta a gaban kotu inda take kalubalantar zaben Buhari, ba tare da ta dumama yanayin siyasar kasar ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel